Dakarun Sojin Sama Sun Yi Luguden Kan Maboyar 'Yan Boko Haram a Borno, Sun Sheke Da Yawa
- Dakarun sojojin saman Najeriya sun yi ɓarin wuta kan maɓoyar ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram a jihar Borno
- Jiragen yaƙin rundunar masu aman wuta sun lalata maɓoyar ƴan ta'addan mai ɗauke da manyan kwamandojinsu
- Manyan kwamandoji da dama ne dai suka sheƙa barzahu yayin wasu daban kuma sha da kyar bayan sun arce ta cikin kogon dutse
Jihar Borno - Ƙungiyar Jama'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wal-Jihad (JAS) ta Boko Haram, ta ƙara shan kashi a hannun dakarun sojin saman Najeriya a jihar Borno.
Jiragen yaƙin dakarun sojin saman sun yi luguden wuta a maɓoƴar ƴan ta'addan da ke a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
Harin an ƙaddamar da shi ne ta hanyar amfani da jiragen Super Tukano a sansanin Ali Ngulde a yankin Arewa maso Gabas na tsaunin Mandara a ranar 6 ga watan Yunin 2023.
Majiyoyi sun tabbatarwa da Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa ƴan ta'adda da dama sun sheƙa barzahu yayin da sauran suka arce ta cikin kogon duwatsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An halaka manyan kwamandojin ƙungiyar
Majiyar ya bayyana cewa jiragen yaƙin sun yi luguden wuta inda suka lalata wani gini mai rufin jan kwano ɗauke da tutar Boko Haram wanda ya zama maɓoyar Ali Ngulde, (Amir Jaysh) na Boko Haram da wasu manyan kwamandoji.
Wasu daga manyan kwamandojin da suka tsere sun haɗa da Ali Ngulde da Muke, yayin da dama daga cikinsu suka gamu da ajalinsu.
Harin wanda na haɗin guiwa ne tsakanin dakaru sojin sama da na na ƙasa, na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan an kai irinsa akan kwamban ƴan ta'addan ISWAP a tsakanin Aulam da Kafa, inda aka halaka da dama daga cikinsu da lalata motocinsu guda biyu.
Dakarun Sojoji Sun Sheke 'Yan Ta'addan ISWAP
A wani labarin na daban kuma, dakarun sojoji sun sheƙe wasu ƴan ta'adda ƙungiyar ta'addanci ta Islamic State For West Africa Povince (ISWAP) a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun sheƙe ƴan ta'addan ne tare da haɗin guiwa ƴan sakai a tsakanin ƙananan hukumomin Chibok da Damboa.
Asali: Legit.ng