Kwanaki 9 da Barin Kujerarsa, Ministan Buhari Ya Sake Samun Wani Aiki Mai Tsoka
- Kamfanin Ballard Partners za su bude ofis a Abuja da Legas bayan shigowarsu nahiyar Afrika
- Har an nada Lai Mohammed a matsayin Manaja, kuma tuni tsohon Ministan ya karbi wannan aiki
- ‘Dan siyasar ya rike Ministan labarai na kusan shekaru takwas gwamnatin Muhammadu Buhari
Abuja – Lai Mohammed wanda ya rike Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya, ya samu aiki da wani kamfanin ketare mai suna Ballard Partners.
A wata sanarwa da Ballard Partners ya fitar a shafinsa na Twitter, an tabbatar da cewa Alhaji Lai Mohammed ya zama daya daga cikin abokan huldarsu.
Bayan shekara da shekaru a Turai da Amurka, wannan kamfani na Duniya ya shigo nahiyar Afrika kuma zai bude ofishinsa a garuruwan Abuja da Legas.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Ballard Partners yana daya daga cikin manyan kamfanonin harkar alaka da gwamnati a kasar Amurka.
Zai bude ofishinsa na farko a Afrika a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Lai Mohammed shi ne tsohon Ministan yada labarai da al’adun Najeriya, zai zama Manajan huldaa ofishin Abuja da kuma ofishin kamfanin da yake Legas.
- Ballard Partners
Dalilin dauko Lai Mohammed
Legit.ng Hausa ta lura an zabi a bude ofisoshin a Abuja da Legas ne kasancewarsu birnin tarayya da garin kasuwanci, Lai ya yi aiki da gwamnatin Legas.
The Cable ta ce shugaban wannan kamfani, Brian Ballard ya zabi Lai Mohammed ne ganin yana cikin jami’an gwamnati da aka fi girmamawa a Najeriya.
Kamar yadda Ballard ya fada, tsohon Ministan mai shekaru 71 ya san kan aiki sosai, saboda haka ake ganin zai taimaka wajen biyan bukatun kamfaninsa.
Da yake magana, tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar APC na-kasa ya nuna farin cikinsa da aka ba shi wannan matsayi, ya na murnar aiki da kamfanin.
‘Dan siyasar yake cewa ya yi murna da kamfanin ya zabi ya bude ofishinsa a Afrika.
Gwamnatin Buhari ta ji kunya
Jirgin saman Nigeria Air da aka gani kwanaki a filin jirgin Abuja ba na gwamnati ba ne, an samu labari cewa ashe hayarsa aka yi tun daga kasar Ethiopia.
Kafin Muhammadu Buhari ya bar ofis, an yi gaggawar shigo da jirgin a lamarin da ya zama dodo-rido. An yi kira ga shugaba Bola Tinubu ya binciki lamarin.
Asali: Legit.ng