Kotu Ta Dakatar da NLC da Wasu Kungiyoyi Daga Shiga Yajin Aiki
- Kotun ɗa'ar Ma'aikata a Abuja ta hana NLC da sauran kawayen ƙungiyar kwadago daga tsunduma yajin aiki ranar Laraba, 7 ga watan Yuni
- Alkalin Kotun ya ɗauki wannan mataki ne yayin yanke hukunci kan bukatar da Ofishin AGF kuma ministan shari'a ya shigar
- Ta ce ba zai yuwu ma'aikata su shiga yajin aiki yayin da daliban Sakandire ke zana jarabawar fita daga matakin Sakandire (WAEC) ba
FCT Abuja - Kotun ɗa'ar ma'aikata mai zama a Abuja ta dakatar da shirin tsunduma yajin aiki wanda ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC) ke yi kan cire tallafin man fetur.
A ranar Litinin, 5 ga watan Yuni, 2023, Alkalin Kotun, mai shari'a Olufunke Anuwe, ya hana NLC da sauran ƙungiyoyin kwadugo shiga yajin aikin da suka tsara.
Alkalin ya haramtawa dukkan ƙungiyoyin tafiya yajin aiki daga ranar 7 ga watan Yuni, har sai Kotun ta yanke hukuncin karshe kan karar da aka shigar gabanta, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Haka nan kuma Kotun ta umarci NLC ta gurfana a gabanta kamar yadda takardar sammaci ta isa ga ƙungiyar a ranar da za'a ci gaba da zaman shari'ar, 19 ga watan Yuni.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kotun ta yanke wannan hukuncin ne kan buƙatar cikin shari'a da Ofishin Antoni Janar na ƙasa (AGF) kuma Ministan shari'a ya nemi dakatar da shirin shiga yajin aikin.
Meyasa Ƙotu ta hana shiga yajin aikin?
Da take bayanin dalilin hana shiga yajin aikin, Kotu ta ce bai dace ƙungiyoyin kwadaho su shiga yajin aiki a halin yanzu ba saboda ɗalibai sun faɗa zana jarabawar fita daga Sakandire (WASSCE).
A jadawalin WAEC, jarabawar ɗalibai ta wannan shekara 2023 ta fara ne daga ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2023da muke ciki, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Gwamnatin Tinubu Ta Kara Shiga Sabon Zama da 'Yan Kadugo a Abuja
A wani rahoton na daban kuma Gwamnatin Najeriya ta ci gaba da zaman tattaunawa da ƙungiyoyin kwadugo kan cire tallafin man fetur.
Taron wanda ya tashi ba tare da fahimtar juna ba ranar Lahadi, 4 ga watan Mayu, 2023, ana tsammanin cimma matsaya a zaman yau Litinin.
Asali: Legit.ng