Kotu Ta Hana Hukumomin EFCC, ICPC Da DSS Daga Cafke Abdul'aziz Yari

Kotu Ta Hana Hukumomin EFCC, ICPC Da DSS Daga Cafke Abdul'aziz Yari

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya samu nasara a kotu kan hukumomin EFCC, ICPC da DSS
  • Wata babbar kotun tarayya a birnin tarayya Abuja, ta hana hukumomin uku daga cafke ɗan takarar shugabancin majalisar dattawa
  • Tsohon gwamnan ya maka hukumomin ƙara a gaban kotun ne domin neman hana su hukumomin yin caraf da shi

Abuja - Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin tarayya Abuja, a ranar Litinin ta hana hukomomin yaƙi da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC, daga tsare Abdulaziz Yari.

Premium Times ta kawo rahoto cewa, kotun ta dakatar da hukumomin daga tsare Abdul'aziz Yari wanda ya ke neman shugabancin majalisar dattawa ta 10, har sai ta kammala sauraron ƙarar da ya shigar a gabanta.

Kotu ta hana EFCC, ICPC da DSS yin caraf da Yari
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari Hoto: Tribune.com
Asali: UGC

Mai shari'a Donatus Okorowo, wanda ya bayar da umarnin kan ƙarar da lauyan Yari, Michael Aondoaaa ya shigar, ya kuma hana rundunar ƴan sandan farin kaya (DSS) daga tsaren zaɓaɓɓen sanatan, rahoton The Nation ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Subhanallahi: Mutane Da Dama Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Kano

Mai shari'ar ya kuma umarci waɗanda ake ƙarar (EFCC, ICPC, DSS) da su kawo hujjoji zuwa ranar da za a ci gaba da sauraron ƙarar, kan dalilin da ya sanya kotun ba za ta amsa buƙatun mai shigar da ƙarar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Saboda haka an hana waɗanda ake ƙarar daga tsare wanda ya shigar da ƙara har sai zuwa ranar da za a ci gaba da sauraron ƙarar." A cewar alƙalin.

Daga nan mai shari'ar ya dage sauraron ƙarar har zuwa ranar 8 ga watan Yuni, domin waɗanda ake ƙarar su kawo dalilansu.

Yari ya buƙaci kotu ta hana hukumomin yin caraf da shi

Tsohon gwamnan na jihar Zamfara, ya shigar da ƙara ta hannun tawagar lauyoyinsa wacce ta haɗa da Abdul Kohol, a ƙarƙashin jagorancin Mr Aondoaaa, a gaban kotun inda ya buƙaci a hana hukumomin guda uku cafke shi.

Kara karanta wannan

Abin Da Buhari Ya Gaza Yi A Shekarunsa 8 Kan Mulki, Mataimakin Shugaban APC Ya Yi Bayani

A cikin ƙarar wacce aka shigar a ranar 2 ga watan Yuni, Yari ya sanya hukumomin EFCC, ICPC da DSS a matsayin waɗanda ya ke ƙara.

Tsohon gwamnan ya buƙaci kotun da ta hana waɗanda ya ke ƙarar daga cafke shi ko barazanar cafke shi, domin hana shi zuwa rantsar da majalisar dattawa ta 10 a ranar 13 ga watan Yunin 2023.

Buhari Ya Ki Goyon Bayan Yari Kan Shugabancin Majalisa

Rahoto ya zo cewa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ƙi nuna goyon bayansa kan kuɗirin Abdulaziz Yari na neman shugabancin majalisar dattawa.

Buhari ya gargaɗi Yari da kada ya bijirewa zaɓin da jam'iyyar APC ta yi kan shugabancin majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng