Tirkashi: ’Yan Sanda Sun Cafke Matar da Ta Damfari Mutane Fiye da 100 Kudi Har N150m
- Jami’an ‘yan sandan jihar Niger sun yi nasarar cafke wata 'yar damfarar mutane, Damilola Akinnowuno
- Ana zargin Damilola da damfarar mutane fiye da 100 a lokuta daban-daban inda kudin ya kai N150m
- Kakakin rundunar a jihar, DSP Abiodun Wasiu ya tabbatar da kama matar inda ya ce ta cutar da mutane da dama
Jihar Niger – Rundunar ‘yan sandan jihar Niger ta kama wata mata mai suna Damilola Akinnowuno da ke unguwar Tunga a cikin Minna babban birnin jihar.
Ana zargin Damilola ne da damfarar mutane da dama makudan kudade har N150m.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya ce damfarar ta kunshi cuta da cin amana da kuma damfara ta yanar gizo wanda aka kawo rahoton ofishin ‘yan sanda a watan Mayu.
'Yan uwan wadda ake zargin sun taimaka wa 'yan sanda
Abiodun ya kara da cewa, wanda ake zargin an kama ta ne da taimakon ‘yan uwanta, kuma a lokacin da ake bincike ta tabbatar cewa tana amfani da kafar yanar gizo don tallata kayan sakawa na mata da jaka da kuma takalma, har ma wayar hannu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
“Binciken farko da muka yi ta tabbatar mana tana fada wa kwastomominta cewa hukumar shige da fice sun kwace kayanta yayin shigo da su Najeriya, sannan ta kama hayan wasu shaguna na N2m don damfarar mutane.
Daily Trust ta tattaro cewa Damilola ta tabbatar da damfarar mutane fiye da 100 makudan kudade da suka kai N150m, Abiodun ya ce yanzu haka mutane 72 sun iso don ba da shaidar damfararsu da ta yi.
An kuma kama wasu matasa bisa zargin kisa
A wani labarin mai kama da wannan, jami’an ‘yan sanda sun kama wani mai suna Bali Joshua dan shekara 33 da kuma Sunday Paul mai shekaru 22 bisa zargin kashe wata mata, Boniface Chinanwa mai shekaru 45 da ke zama a Suleja, cewar rahotanni.
Yayin gabatar da su masu laifin, Abiodun ya ce sun tabbatar da aikata laifin da ake tuhumarsu akai, inda ya ce a watan Mayu wani mai suna Zingfa Selchak wanda har yanzu ba a san inda yake ba ya kira su da su taimaka masa ya kwace wata adaidaita sahu.
Wani Mutum Ya Damfari Yar Gidan Magajiya A Abuja, Bai Biya Ta Kudin Aiki Ba
A wani labarin, wata kotu da ke zamanta a Dei-Dei na zargin matashi Victor Emeka bisa cin amana da kuma damfara.
Kotun ta ba da umarnin tasa keyarsa zuwa gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Asali: Legit.ng