Talaka Zai Samu Sauƙi, ‘Yan Kasuwa Sun Ce Farashin Man Fetur Zai Sauko Ƙasa
- Kungiyar ‘yan kasuwa ta IPMAN tayi wa ‘Yan Najeriya albishir da cewa farashin fetur zai sauka
- Shugaban IPMAN na reshen Enugu ya ce yanzu ‘yan kasuwa za su fara tsere da junansu a kasar
- A karshe Chinedu Anyaso ya nuna fetur zai sauko domin kowa zai so farashinsa ya karkato mutane
Anambra - Kungiyar ‘yan kasuwan mai wadanda aka fi sani da IPMAN ta yabawa gwamnati a kan amincewa da ta yi a rika shigo da mai daga waje.
The Guardian ta rahoto Mista Chinedu Anyaso wanda shi ne shugaban kungiyar IPMAN na tashar Enugu ya yi maraba da sabon mataki da aka dauka.
Chinedu Anyaso ya yi magana a garin Awka da ke jihar Anambra a ranar Lahadi, ya na ganin an yi daidai da aka ba ‘yan kasuwa damar shigo da mai.
Anyaso ya na ganin ba ‘yan kasuwa dama da hukumar NMDPRA tayi, zai kawo cigaba a maimakon a bar wuka da nama ga kamfanin NNPC kadai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Amfanin bada lasisi ga 'yan kasuwa
A cewar shugaban na IPMAN, hakan zai jawo ‘yan kasuwa su rika tsere da junansu wajen jawo abokan ciniki, sannan za a bar kasuwa ta tsaida farashi.
Kwanaki biyu da suka wuce, na nanata kira ga gwamnatin tarayya da ta bada lasisi ga ‘yan kasuwa.
Na fada cewa kuskure ne a ce NNPCL wanda kamfanin ‘yan kasuwa ne shi ne kadai zai shigo da mai kuma ya tsaida farashin da za a a saida.
Nayi farin ciki da hukumar NMDPR A ta bada sanarwa cewa an ba ‘yan kasuwa dama. Haka ya kamata idan dai gwamnati ta cire hannunta.
Takarar da za a fara a ‘yan kwanakin nan masu zuwa zai kauda radadin karin fashin kayan man.
- Chinedu Anyaso
Daily Trust ta ce Mista Anyaso ya bukaci gwamnati tayi kokarin ganin an gyara matatun gwamnati, kuma a bada lasisin kafa wasu kananan matatu.
Shugaban na IPMAN shi ne mai kula da tashoshin man da ke jihohin Anambra, Ebonyi da Enugu.
Fetur zai karye?
Ana yada cewa idan Aliko Dangote ya fara tace mai, mutane za su saye fetur a gidan mai da araha, an samu rahoton da ya yi karin haske a kan lamarin.
Shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari ya ce tace mai a Najeriya bai nufin samun rahusa a farashi kuma an ji inda 40% na fetur din da ake sha su ke tafiya.
Asali: Legit.ng