Tinubu Ya Nada Ribadu a Matsayin Mai Ba Shi Shawari Kan Harkokin Tsaro? Shehu Sani Ya Magantu

Tinubu Ya Nada Ribadu a Matsayin Mai Ba Shi Shawari Kan Harkokin Tsaro? Shehu Sani Ya Magantu

  • Shehu Sani ya yi alama da cewa an nada Nuhu Ribadu a matsayin sabon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA)
  • Tsohon dan majalisar ya ce nadin da ake zargin an yiwa Ribadu, wanda tsohon shugaban hukumar EFCC ne abin yabawa ne
  • A cewar Sani, Ribadu bai samu wani mukami ba a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin shi ba “Dan a mutun Buhari” bane

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta 8, Sanata Shehu Sani, ya bayyana alamar haske cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Nuhu Ribadu a matsayin sabon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA).

Legit.ng ta lura cewa shugaba Tinubu bai bayyana nadin Ridabu a matsayin NSA a hukumance ba.

Kara karanta wannan

Ya samu raguwar arziki: Buhari ya gama mulki, ya fadi adadin dukiyar da ya mallaka yanzu

Da gaske an nada Ribadu a mulkin Tinubu?
Sani, Ribadu da Tinubu | Shehu Sani/Nuhu Ribadu/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Abin da yasa ba a ba Ribadu mukami a mulkin Buhari ba

Sani ya ce zargin da ake cewa an nada Ribadu a matsayin NSA abin yabawa ne kuma ya yi ikirarin cewa ba a ba tsohon Shugaban na EFCC ba mukami a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin shi “Dan a mutum Buhari” bane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuni, a shafinsa na Twitter @ShehuSani.

Tsohon dan majalisar ya rubuta:

“Nada Nuhu Ribadu a matsayin sabon NSA abin yabawa ne. Ina sane da muhafikai da mahassadan da suka tabbatar an hana Ribadu wani mukami a shekaru takwas da suka wuce saboda ba dan A mutun Buhari bane. Kalubalen da ke gabansa shine magance matsalolin tsaro. Ina yi masa fatan alheri.”

Ba wannan ne karon farko da Shehu Sani ke bayyana hasashensa game da gwamnatocin kasar nan ba, ya sha yin hasashe da yawa, amma abin tambayan, shin hasashen nasa ka iya zama gaskiya kuwa?

Kara karanta wannan

“Sai An Tauna Tsakuwa Idan Za a Kai Najeriya Gaba”: Wike Ya Goyi Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Mai

Tinubu ya ba Femi Gbajabiamila matsayin shugaban ma’aikatansa

A wani labarin, kunji yadda rahotanni suka karade kasa cewa, Femi Gbajabiamila ya zama shugaban ma’aikatan shugaban kasa Bola Tinubu.

Wannan na zuwa ne bayan da aka rantsar da Tinubu a mulkin Najeriya a watan da ya gabata na Mayu.

Majiya ta bayyana cewa, Tinubu ya Femi wannan mukamin ne tare da bayyana wasu sauran da ya amince da nadinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.