Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Shiga Taro Da Kungiyar Kwadago Kan Cire Tallafin Man Fetur

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Shiga Taro Da Kungiyar Kwadago Kan Cire Tallafin Man Fetur

  • Gwamnatin tarayya ta shiga zama da ƙungiyar ma'aikata ta ƙasa kan cire tallafin man fetur da aka yi a ƙasar nan
  • Zaman wanda shi ne na biyu bayan ɓangarorin sun zauna a satin da ya gaɓata kan batun janye tallafin man fetur ɗin
  • A zaman na yau ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) wacce ta yi barazanar shiga yajin aiki, ba ta halarce shi ba

Abuja - Wakilan gwamnatin tarayya za su yi zama da wakilan ƙungiyar ma'aikata ta ƙasa (TUC), a yammacin yau Lahadi a fadar shugaban ƙasa kan cire tallafin man fetur, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.

Taron na su na zuwa ne kwanaki biyar bayan zaman da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu, an tashi baram-baram.

Gwamnatin tarayya ta shiga taro da kungiyar ma'aikata ta kasa (TUC)
Gwamnatin tarayya na ganawa da kungiyar TUC kan cire tallafin man fetur Hoto: Tribune.com
Asali: UGC

Shugaban ƙasa Bola Tinubu a lokacin jawabinsa bayan an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, ya sanar da cewa tallafin man fetur ya tafi kenan

Kara karanta wannan

Kalubale 10 Masu Hadari Da Tinubu Ya Tsallake Kafin Shiga Fadar Shugaban Kasa

Wannan furucin da shugaban ƙasar ya yi, ya sanya an samu dogayen layuka a gidajen siyar da man fetur, inda nan da nan farashin man fetur ɗin ya yi tashin gwauron zaɓi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A lokacin wancan zaman na farko, shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) Joe Ajaero da takwaransa na ƙungiyar ma'aikata (TUC), Festus Osifo, sun bayyana cewa dole ne gwamnati ta koma kan wancan tsohon farashin man fetur ɗin ko su tsunduma cikin yajin aiki a ranar Laraba mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ba ta halarci zaman ba

A zaman na yau Lahadi wanda aka fara da misalin ƙarfe 5 na yamma, ƙungiyar ƙwadago ba ta samu halartar zaman ba, cewar rahoton Channels Tv.

Wakilan gwamnatin tarayya a wajen taron sun haɗa da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele, shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) Mele Kyari da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole.

Kara karanta wannan

“Gwamnati Mai Ci A Yanzu Ta Wucin Gadi Ce, Zan Karbo Kujerata a Kotu”, Atiku Abubakar

Sauran sun haɗa da babban sakataren national sugar development council (NSDC), Zacch Adedeji, mataimakin shugaban NNPCL, Yemi Adetunji, tsohon kwamishinan watsa labarai na jihar Legas, Dele Alake, James Faleke da sauransu.

A ɓangaren TUC akwai wakilai guda bakwai a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Festus Osifo.

Kawunan Kungiyar Kwadago Sun Rabu a Dalilin Yajin Aiki

Rarrabuwar kawuna ta shiga cikin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) kan yajin aikin da ta ke shirin tsunduma a dalilin cire tallafin man fetur.

Rassan ƙungiyar na yankunan Arewa da Kudu maso Yamma, sun janye daga shiga yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng