“Hankalina Ya Fara Tashi”: Wata ’Yar Najeriya Ta Zubar da Kwallo a Cikin Wani Bidiyon Bayan Ta Yi Aure

“Hankalina Ya Fara Tashi”: Wata ’Yar Najeriya Ta Zubar da Kwallo a Cikin Wani Bidiyon Bayan Ta Yi Aure

  • Wata mata ‘yar Najeriya ta zo kafar sada zumunta, inda ta bayyana yanayin da take ciki a rayuwarta da wani dan jihar Anambra
  • Ta zubar da kwalla, inda ta yi korafin cewa, ta fara samun matsalar kwakwalwa inda ta nemi shawarin wasu matan na daban
  • Mutane da yawa sun ba ta shawari, inda suka bayyana yadda suke rayuwa da kuma yadda suke magance matsaloli

Wata mata ‘yar Najeriya mai suna Ada Gold ta fashe da kuka a kafar sada zumunta kan yadda aure ke ba ta wahala.

Matar wacce tace ita ‘yar asalin jihar Imo ce ta auri wani dan jihar Anambra, amma hadin nasu kamar akwai kitimurmura da yawa a ciki.

A wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta, an gano lokacin da Ada ke zubar da kwalla tare da tambayar matan da ke aure a Anambra kan yadda suke ji da mazajensu.

Kara karanta wannan

Tsadar mai: Kungiyar 'yan jarida ta tubure, ta ce za ta yi gagarumar zanga-zanga a Najeriya

Daga aure, ta shiga tashin hankali
Matar da ta yi aure a Anambra ta shiga tashin hankali | Hoto: @adagold49
Asali: TikTok

Ta tambaye su kan yaya suke ji da mazajensu, inda ta kara da cewa, ita fa ta rasa yadda za ta yi, ta ma fara birkicewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamanta:

“Don Allah 'yan matan jihar Imo da ke auren mazan Anambra yaya kuke fama ne."

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a game da bidiyon

teashabella56:

“Mazan Anambra na da mutunci da mutuntawa da kyau kuma suna da alfahari don haka na gudu da kafa ta kiyi hakuri ‘yar uwa”

regyneye:

“Yana da kyau yadda aka alanta mazan Anambra da haka, bari ki ji ba batu bane na jiha kawai dai kin yi gamo ne.”

amarahappy175:

“Baki ga alama bane kafin ki shiga? Babu yadda za a yi ki fara nema da wani ba tare da sanin idan kika aure shi ba za ki ji dadi ba a ranki.”

Kara karanta wannan

Tun Yanzu Wasu Kungiyoyi 3 Sun Fito Za Su Yaki Bola Tinubu Kan Cire Tallafin Fetur

bella:

“A gani na Anambra bata da laifi kawai dai ahalin da kika yi aure ne ki juya dan uwansu.”

ikeomumu favour chiamaka:

“Malama ki bar batun jiha kawai irin mutumin da kika aura ne, kada ki yi kuka ki yi hakuri.”

@perkylove:

“Ina jin dadi na
“Mijina na min abin da nake so.
“Matan da mazajensu ke abu kamar yara ne ke shan wahala.
“Mijina ya san abin da yake.”

Maya:

“Na auri mutumin Anambra kuma ina jin dadin zaman, ‘yar uwata mutumin da kika aura ne kawai ba jihar ba da kika yi aure ba amma aure a Anambra akwai dadi.”

Wata budurwa kuwa, ta ce ta daina aikin assha, ta mika rayuwarta ga Yesu Al-masihu, bata yi bayanin aure ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.