Tallafin Fetur: NNPC Ya Fadi Sabon Shirin Bola Tinubu Tun da Farashi Ya Kai N550
- Mele Kolo Kyari ya yi wa manema labarai bayanin halin da ake ciki a game da tallafin man fetur
- Shugaban kamfanin na NNPCL ya ce Bola Tinubu ya yi umarni a fito da wasu sababbin tsare-tsare
- Wadannan tsare-tsare za su taimakawa talakan kasar nan ya samu sa’ida a kan tsadar da fetur ya yi
Abuja - Shugaban kamfanin mai na kasa watau NNPCL, Mele Kolo Kyari, ya shaida cewa za a dauki mataki a game da cire tallafin man fetur.
A ranar Alhamis, This Day ta rahoto Mele Kolo Kyari ya na cewa Bola Tinubu ya yi umarni a samar da tsare-tsare da za su rage zafin janye tsarin.
Malam Mele Kyari ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wajen ‘yan jarida bayan zama da shugabannin jam’iyyar APC.
Kyari ya kuma shaida cewa ba za ta yiwu a ce kamfanin NNPCL kadai yake shigo da mai ba. Wannan labari ya zo a jaridar nan ta Leadership a jiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wa zai rika shigo da mai?
"Za a bi sannu a hankali har ta kai ana bada kudin kasashen waje ga kowane mai bukatar su shiga kasashen Duniya domin su shigo da mai cikin Najeriya.
Kuma NNPC ba za ta cigaba da zama kamfani tilo da yake shigo da mai a kasar nan ba. Mun san za a kawo karshen wannan, kasuwar za ta mike da kan ta."
- Mele Kolo Kyari
Gyaran matatun gwamnati
Game da gyara matatun da ake da su, Kyari ya ce yanzu ana gyara wata matatar kuma zai fara aiki a shekarar nan, sauran za su dawo aiki a 2024 da 2025.
An kai matsayin da ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya ba za ta iya cigaba da biyan tallafn fetur ba, NNPCL GMD ya ce hakan ya jawo dole a cire shi.
A madadin hakan, sabon shugaban kasa ya yi umarni a samar da hanyoyin da za a ragewa talaka radadi a dalilin tashin da farashin man fetur ya yi a Najeriya.
"Ina da labari Ma girma shugaban kasa (Bola Tinubu) ya yi umarni a samar da wasu tsare-tsare da wasu shirye-shriye, kuma na tabbata za ayi hakan."
- Mele Kolo Kyari
A rahoton, Kyari bai yi bayanin irin abubuwan da za a fito da su a madadin tallafin fetur ba.
Babu mamaki gwamnatin tarayya ta samar da motocin haya masu rahusa domin talakawa ko kuma ayi kokarin shigo da motocin da ba su amfani da fetur.
Ayi Fayose ya yaba
Game da cire tallafin fetur, rahoto ya zo Ayodele Fayose ya na cewa ya yi imani shugaban kasa watau Bola Tinubu ya dauki matakin da ya dace.
Fayose ya yi kira ga mutanen Najeriya su yi hakuri da gwamnatin nan domin wahalar da aka shiga za ta tafi, ya ce Gwamnatin baya ce tayi barna.
Asali: Legit.ng