Alhazan Jigawa Sun Sake Komawa Kano Bayan Jirgin Da Aka Sauya Masu Ya Samu Matsala
- Alhazan jihar Jigawa sun sake dawowa Kano bayan jirgin da aka sauya masu ya sake samun matsala
- A ranar Laraba, 31 ga watan Mayu ne jirgin da zai yi jigilar alhazan Jigawa zuwa Saudiyya ya yi saukar gaggawa a Kano bayan walkiya ta taba gilashin gaban jirgin
- An sauya masu wani jirgi kuma har sun tashi amma suka juyo bayan sun kai kasar Kamaru sakamakon wata matsala da ta sake samun jirgin
Jirgin sama na kamfanin Max Air da ke dauke da masu zuwa aikin hajji daga jihar Jigawa ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke jihar Kano karo biyu a jere.
Idan za ku tuna, mun kawo a baya cewa jirgin ya yi saukar gaggawa bayan walkiya ta taba hancinsa a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu.
Sai dai kuma, jaridar Aminiya ta rahoto cewa jirgin da aka musanyawa alhazan wanda ya tashi da misalin karfe 2:00 na dare ya dawo Kano da misalin karfe 5:40 na asuba a ranar Alhamis sakamakon wata matsala da ya samu.
Jirgin alhazan ya samu matsala a hanyar Kamaru sai suka jiyo Kano, Majiya
Wata majiya ta bayyana cewa jirgin ya samu matsala ne a kan hanyarsa ta kasar Kamaru, lamarin da ya tilasta masa dawowa Kano.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar wani ma'aikacin filin jirgin sama na Kano da ya nemi a boye sunansa, alhazan suna nan suna jiran jirgin da zai kwashe su.
Ya ce:
“A yanzu ga su nan a kasa, jirgin da ya fara diban su daga Dutse tuni aka gyara, shi wanda za a yi amfani da shi wajen kwashe alhazan."
Wata daga cikin alhazan ta bayyanawa jaridar cewa a yanzu haka ana shirye-shiryen sanya su a wani jirgin,
Mahajjaciyar ta ce:
“Har mun isa kasar Kamaru sai aka sake juyawa da mu, an sanar da mu cewa shi ma wannan jirgin ya samu matsala. Sai dai ba su sanar da mu matsalar ba. A yanzu haka dai ana shirye-shiryen sake zuba mu a wani jirgin.”
Kamfanin Max Air ta yi martani
Manajan kamfanin jirgin na Max Air a Kano, Bello Ramadan ya tabbatar da cewar jirgin na biyu ya dawo filin jirgin sama na Kano bayan ya samu yar matsala, Premium Times ta rahoto.
Sai dai kuma, Mista Bello bai bayyana matsalar da aka samu ba. Ya ce an samar da wani jirgi domin jigilar alhazan, kuma cewa za su tashi zuwa Saudiyya nan gaba kadan a yau Alhamis.
Jirgin alhazan Jigawa ya yi saukar gaggawa a Kano
A baya mun kawo cewa wani jirgin sama mai tafiya kasar Saudiyya ya tsallake rijiya da baya inda ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano bayan injin dinsa ya samu matsala a sama.
Jirgin na kamfanin Max Air Limited da lamba, Max B747-HMM yana dauke da rukunin farko na maniyyata aikin hajji 554 daga garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa zuwa Saudiyya domin aikin hajjin 2023.
Asali: Legit.ng