"Ba Na Son Kawunanku Su Rabu a Karkashin Mulkina": Tinubu Ƴa Gargadi Hafsoshin Tsaro

"Ba Na Son Kawunanku Su Rabu a Karkashin Mulkina": Tinubu Ƴa Gargadi Hafsoshin Tsaro

  • Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike da muhimmin gargaɗi kan hafsoshin tsaro na hukumomin tsaro na ƙasar nan
  • Shugaba Tinubu ya gargaɗe su cewa ba zai lamunci rashin haɗa kai ba a tsakanimsu a ƙarƙashin gwamnatinsa
  • Shugaban ƙasar ya kuma yaba musu kan yadda nasarorin da suka samu a baya inda ya sha alwashin ɗorawa akan hakan

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya buƙaci manyan hafsoshin tsaro da su yi aiki tare domin ƙara ƙarfafa faɗan murƙushe matsalar tsaro a ƙasar nan.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa, Tinubu ya bayar da wannan gargaɗin ne a yayin zaman da ya yi da manyan hafsoshin tsaro na ƙasar nan a ranar Alhamis, 1 ga watan Yunin 2023.

Tinubu ya ja kunnen hafsoshin tsaro
Shugaba Tinubu da Babagana Monguno bayan kammala taron Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Da ya ke tattaunawa da ƴan jaridar fadar shugaban ƙasa bayan taron, mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Babagana Monguno, ya ce shugaban ƙasar ya ɓuƙaci su riƙa tattauna a tsakaninsu a ko da yaushe.

Kara karanta wannan

Wasu Muhimman Bukatu Da Kungiyar Dattawan Arewa Ta Mika Zuwa Ga Shugaba Tinubu

Shugaban ƙasar ya kuma umarci hukumomin tsaron da su samar da tsari mai kyau, kan yadda za a kawo ƙarshen satar ɗanyen mai da ake fama da ita a ƙasar nan, cewar rahoton The Cable.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Monguno ya bayyana cewa:

"Shugaban ƙasa ya bayyana cewa, domin ciyar da ƙasar nan gaba, dole ne jami'an tsaro su ƙara zage damtse. Sannan ya kuma yi nuni da cewa falsafarsa itace ɗaukar matakan da suka dace da zamani domin kawo ƙarshensu."

Tinubu ya shirya ba su dukkanin goyon bayan da suke buƙata

Monguno ya kuma bayyana cewa shugaban ƙasar a lokacin zaman da suka yi na tsawon sa'o'i biyu da hafsoshin tsaron, ya gaya musu cewa a shirye ya ke ya ɗora daga nasarorin da aka samu, da magance koma bayan da aka samu domin amfanin ƙasa.

Kara karanta wannan

Abin Da Buhari Ya Gaza Yi A Shekarunsa 8 Kan Mulki, Mataimakin Shugaban APC Ya Yi Bayani

Ya kuma ƙara da cewa Tinubu ya ce bai kamata ƙasar nan na rarrafe ba yayin da sauran ƙasashe na tafiya suna ƙara samun haɓɓaka.

Waɗanda suka halarci zaman na farko tsakanin shugaban ƙasan da hafsoshin tsaron sun haɗa da, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya, babban hafsan sojojin ruwa, V. Admiral Awwal Gambo.

Sauran sun haɗa da babban hafsan sojojin sama, Air Marshal Isiaka Amao, da kuma sufeto-janar na ƴan sanda, Usman Alkali Baba.

Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Tsaro a Villa

Da zu rahoto ya zo cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya sanya labule da shugabannin tsaro a fadarsa da ke Aso Rock Villa.

Wannan ganawar dai ita ce ta farko tun bayan da aka rantsar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng