Tsohon Gwamnan PDP Ya Yabi Tinubu, Mutane Ana Kuka da Janye Tallafin Fetur
- Ayodele Fayose ya ce a kan batun janye tallafin man fetur, lallai ya na goyon bayan Bola Ahmed Tinubu
- Tsohon Gwamnan Ekiti ya ce sabuwar gwamnati tayi daidai wajen yin gaggawar fatali da tsarin tallafin man
- Fayose ya yi kira ga mutanen Najeriya da kungiyar NLC su hakura da matakin da aka dauka domin gyara kasa
Lagos - Ayodele Fayose wanda ya yi Gwamna sau biyu a jihar Ekiti, ya tofa albarkacin bakinsa bayan gwamnatin tarayya ta janye tsarn tallafin man fetur.
A daidai lokacin da mafi yawan mutane su ke wayyo da matakin da Bola Ahmed Tinubu ya dauka, Vanguard ta ce Ayodele Fayose ya yabi shugaban kasar.
A yayin da ya ke magana a shafinsa na Twitter, Fayose ya ce sabon shugaban Najeriya ya dauki matakin da ya dace wanda zai taimaki ‘yan Najeriya.
Tsohon Gwamnan ya ke cewa ba za a dade ana shan wahala ba, za a ji dadin matakin da aka dauka, har ya kuma bada shawarar hukunta masu boye fetur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganar Ayo Fayose
"A game da cire tallafin man fetur, na yi imani shugaban kasa (Bola) Tinubu ya dauki matakin da ya fi dacewa.
Hakan shi ne daidai ga Najeriya da mutanenta. Dama ya yi alkawari zai janye tallafin (fetur), bai taba boyewa ba.
Abu mafi muhimmanci shi ne, gwamnatin da ta wuce ta janye tallafin, tun da ba ta sa shi a kasafin kudin 2023 ba.
Ina kira ga 'Yan Najeriya su yi hakuri da gwamnatin nan domin wahalar da aka shiga za ta tafi bayan wani lokaci.
- Ayo Fayose
Fayose ya ce cire tallafin man fetur shi ne abin da ya fi dacewa ayi, kuma an yi gaba daya an huta, a cewarsa ba talaka ne yake cin moriyar tsarin nan ba.
Kira ga jama'a da NLC
“Gwamnatoci da-dama sun zo sun yi zakin baki da abubuwan nan, lokaci ya yi da za a ceci kasarmu ta hanyar daukar matakai da za a iya ganin masu zafi.
NLC da sauran masu ruwa da tsaki musamman talakan Najerya su fahimci gwamnatin baya tayi barna, sai dai wannan gwamnati ta nemi hanyar gyara.”
- Ayo Fayose
Ina kudin SWV su ka shiga?
An ji rahoto cewa Majalisa ta ce Naira Tiriliyan 3.8 suka yi kafa a ma’aikatun tarayya tsakanin 2017 da 2021, wani bincike kwamitin Sanatoci ya nuna haka.
Binciken Sanatoci ya nuna an yi facakar ne a NACA, NECO, NSCDC, FERMA da NEMA. Sauran inda aka tafka badakalar sun hada da DMO, NAHCON, NAFDAC.
Asali: Legit.ng