Yanzu Yanzu: Jirgin Mahajjata Daga Jigawa Ya Yi Saukar Gaggawa a Kano

Yanzu Yanzu: Jirgin Mahajjata Daga Jigawa Ya Yi Saukar Gaggawa a Kano

  • Jirgin sama dauke da rukunin farko na alhazan jihar Jigawa ya tsallake rijiya da baya a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu
  • Jirgin na kamfanin Max Air mai lamba Max B747-HMM da ya taso daga Dutse, babban birnin jihar Jigawa ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano
  • Hakan ya kasance ne sakamakon ruwan sama da aka yi inda walkiya ta taba gilashin gaban jirgin

Kano - Wani jirgin sama mai tafiya kasar Saudiyya ya tsallake rijiya da baya inda ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano bayan injin dinsa ya samu matsala a sama a yammacin ranar Laraba, 31 ga watan Mayu.

Jirgin na kamfanin Max Air Limited da lamba, Max B747-HMM yana dauke da rukunin farko na maniyyata aikin hajji 554 daga garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa zuwa Saudiyya domin aikin hajjin 2023.

Kara karanta wannan

Matakalar Taron Rantsar da Abba Gida Gida Ta Rushe Yayin Bikin Rantsar da Shi a Kano

Jirgin kamfanin Max Air
Yanzu Yanzu: Jirgin Mahajjata Daga Jigawa Ya Yi Saukar Gaggawa a Kano Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jirgin wanda ya bar filin jirgin saman na Dutse a jihar Jigawa ya dakatar da tafiyarsa zuwa kasar Saudiyya lokacin da walkiya ta same shi inda hakan ya shafi hancin jirgin.

Wata majiya a filin jirgin saman wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce ana kan gyara jirgin kuma an ajiye maniyyatan a filin jirgin har zuwa karfe 8:00 na dare.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce tawagar injiniyoyi na kamfanin na aiki don daidaita lamarin yayin da matsalar ta shafi hancin jirgin ne kawai.

Majiyar ta ce:

"Eh da gaske ne. Sun sauka a nan kuma yanzu haka da nake magana da kai, injiniyoyi na aiki don gyara jirgin. Ya samu matsala ne a hancinsa. Wasu muhimman abubuwa sun bata yayin da wasu suka lalace saboda wani dalili da ba a sani ba tukuna.

Kara karanta wannan

Cika aiki: Saura sa'o'i ya sauka, El-Rufai ya haramta wata kungiya a Kaduna

"Yanzu haka suna cire wasu kayayyaki da suka baci sannan ana sauya su da wasu."

Hakazalika, wata daga cikin fasinjojin jirgin ta tabbatar da lamarin ga Daily Trust cewa an bukaci da su ci gaba da kasancewa a cikin jirgin yayin da ake shirye-shiryen daukarsu zuwa kasar Saudiyya.

Ta ce lamarin ya afku ne sakamakon ruwan sama da aka yi.

Ta yi bayani:

"Yayin da muke kan tafiya, ba mu ma lura da akwai matsala ba. Daga baya sai suka bayar da sanarwa cewa dole mu yi saukar gaggawa a Kano. Muna ciki yanzu haka, za su sauya mana wani jirgin. Abun da suka ce kenan."

Walkiya ce ta taba gilashin gaban jirgin, manajan Max Air

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Manajan kamfanin Max Air a Kano, Bello Ramadan, ya sanar da ita cewa jirgin ya bukaci sauka a filin jirgin sama na Kano ne bayan walkiya ta taba gilashin gabansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng