Yanzu Yanzu: Kungiyar Kwadago Ta Yi Watsi Da Sabon Farashin Man Fetur

Yanzu Yanzu: Kungiyar Kwadago Ta Yi Watsi Da Sabon Farashin Man Fetur

  • Kungiyar kwadago ta kasa ta dauki dumi yayin da kamfanin NNPCL Ya sanar da kara farashin man fetur
  • Kakakin NLC, Garba Deen Muhammad ya ce wannan ba abun yarda bane inda ya yi kira ga FG da ta gaggauta umurtan NPPC da ta janye sabon farashin
  • Kungiyar NLC ta ce wannan mataki da gwamnati ta dauka kamar dabawa yan Najeriya wuka ne

Abuja - Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi watsi da sabon farashin man fetur da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya sanar.

Dairy Trust ta rahoto cewa kamfanin man fetur din ya bukaci gidanjen mansa da ke fadin kasar da ya siyar da man fetur tsakanin N480 da N570 kan kowace lita daya.

Bututun man fetur
Yanzu Yanzu: Kungiyar Kwadago Ta Yi Watsi Da Sabon Farashin Man Fetur Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Garba Deen Muhammad, babban jami'in hulda da jama'a na kamfanin NNPC, ya bayyana cewa an sauya farashin man ne daidai da yadda tsarin kasuwa yake.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Sanatocin PDP Guda Biyu Sun Yi Murabus, Sun Fice Daga Jam'iyyar

Sai dai kuma, shugaban kungiyar kwadago ta kasa, Kwarad Joe Ajaero, wanda ya zanta da manema labarai a Labour House da ke Abuja a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu, ya ce kungiyar ba za ta yarda da hakan ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewar kayyade farashin ba abu ne da gwamnati za ta iya yi ita kadai ba.

Kara farashin mai zai kawo cikas ga tattaunawa da masu ruwa da tsaki a bangaren mai

Da yake bayyana ci gaban a matsayin abun takaici, Ajaero ya ce matakin da NNPCL ya dauka na zuwa ne yayin da ake kan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a bangaren mai da gas iskar gas don magance lamarin amma sai ga sanarwa daga shugaban, rahoton Channels TV.

Wani bangare na sanarwar da Ajaero ya fitar na cewa:

“Wannan ba abun yarda bane kuma muna Allah wadai da shi matuka. Tattaunawa da zuciya daya shine hanyar cimma yarjejeniya. Abun da gwamnati ta yi kamar rike bindiga ne a daidai kan mutanen Najeriya da kawo matsin lamba ga shugabanni wanda zai kawo karan tsaye ga tattaunawar.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya su Shirya, NNPC Ya Kara Farashin Man Fetur a Duk Gidajen Mai da Ke Karkashinsa

"Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta umurtan NNPC da ta janye wannan farashin domin ba bangarorin damar tattaunawa. Yan Najeriya ba za su yarda da magudi kowani iri daga kowani bangare ba musamman daga wakilan gwamnati."

NNPC Ya Kara Farashin Man Fetur a Duk Gidajen Mai da Ke Karkashinsa

A baya mun kawo cewa kamfanin NNPC ya tabbatar da kara farashin litar man fetur a gidajen mayin da suke karkashinsa.

A wata sanarwa ta kamfanin ya fitar a ranar Laraba 31 ga watan Mayu ta bakin kakakin kamfanin, Garba Deen Muhammad ya ce karin farashin ya yi daidai da yadda tsarin kasuwa yake a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng