Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Shugaban Hukumar EFCC a Abuja
- Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya sanya labule da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasa (EFCC) a birnin tarayya Abuja
- Shugaban Tinubu ya gana da Abdulrasheed Bawa ne a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa a ranar Talata da rana
- Ganawar su ba ta rasa nasaba da taƙaddamar da ta auku tsakanin hukumar EFCC da hukumar DSS a jihar Legas
Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanya labule da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa, a birnin tarayya Abuja, rahoton Punch ya tabbatar.
Ganawar ta su na zuwa ne ƙasa da sa'o'i 24 bayan shugaba Tinubu ya bayar da umarni ga hukumar ƴan sandan fararen kaya (DSS) da ta fice daga ofishin hukumar EFCC na Ikoyi da ke jihar Legas.
Bawa, wanda ya isa fadar shugaban ƙasar bayan ƙarfe 2:00 na rana, an yi masa iso zuwa ofishin shugaban ƙasa.
Duk da dai, ba a bayyana dalilin ganawar ta su ba, ganawar ta su ba ta rasa nasaba da hargitsin da ke a tsakanin hukumar EFCC da rundunar DSS.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaba Tinubu a ranar Talata, ya umarci jami'an hukumar DSS da su gaggauta ficewa daga ofishin hukumar EFCC na Ikoyi a jihar Legas.
Shugaban ƙasar ya bayar da wannan umarnin ne bayan rahoto ya iso masa cewa jami'an DSS sun dira a ofishin na EFCC da ke a kan hanyar Awolowo a Ikoyi, ranar Talata, inda suka hana jami'an EFCC shiga cikin ofishin.
Hukimomin biyu sun yi magana kan taƙaddamar
Da aka tuntuɓi kakakin hukumar EFCC. Wilson Uwujaren dangane da lamarin, ya bayyana cewa abin ya yi masa banbarankwai saboda hukumomin biyu sun zauna a gini tare fiye da shekara 20 ba tare da wata matsala ba a tsakaninsu.
Sai dai da ya ke mayar da na sa martanin, kakakin hukumar DSS ya bayyana cewa ginin da aka magana akai na hukumar DSS ne, saboda haka kuskure ne a ce jami'anta sun mamaye ofishin EFCC, cewar rahoton Daily Trust.
Shehu Sani Ya Fallasa Sirrin El-Rufai
A wani labarin na daban kuma, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana zaman jiran samun muƙami mai gwaɓi a gwamnatin Tinubu.
Shehu Sani ya kuma ƙalubalanci El-Rufai da ya gayawa duniya kadarorin da ya mallaka idan har ya isa.
Asali: Legit.ng