Arzikin Dangote Ya Yi Tashin Gwauron Zabi, Ya Koma Cikin Jerin Hamshakan Attajirai 70 a Duniya
- Aliko Dangote ya ƙara matsawa da matsayi tara a cikin jerin hamshaƙan attajiran duniya, inda ya koma na matsayi na 75
- Hakan ya faru ne biyo bayan samun $769m da hamshaƙin attajirin ya yi a ranar Talata, 30 ga watan Mayun 2023
- Haka kuma, dukiyarsa ta yi tashin gwauron zabi daga $20.5bn zuwa to $21.2bn cikin sa'o'i 24 saboda zuba hannun jari a kamfanin simintinsa
Hamshaƙin attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya tsallake matakai tara inda ya koma na 75 a cikin jerin attajiran duniya daga mataki na 84 da ya ke da a baya a ranar Talata, 30 ga watan Mayun 2023.
Hamshaƙin attajirin ya kwashe kusan fiye da shekara ɗaya a matsayin da ya baro a baya, kafin ya samu wannan babbar nasarar a ranar Laraba, 31 ga watan Mayun 2023.
Dukiyar Dangote ta ƙaru da $769m
A cewar ƙididdigar attajirai ta Bloomberg, dukiyar hamshaƙin attajirin ta ƙaru da $769m a cikin kwana ɗaya, inda yanzu ta ke a $21.2bn daga $20.5bn da ta kwashe har na tsawon wata huɗu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dangote, wanda ya ƙaddamar da matatar man fetur ɗin sa mai ƙarfin tace gangar mai 650,000 a rana ɗaya, a ranar 22 ga watan Mayun 2023, ya samu wannan tagomashin ne a dalilin kamfanin simintinsa.
An yi cinikayyar hannun jarin kamfanin simintin Dangote akan N290 a ranar Talata, 30 ga watan Mayu, bayan masu zuba hannun jari sun yi rububinsa.
Hamshaƙin attajirin ya kuma bayyana cewa matatar man fetur ɗin sa za ta fara fitar da kayayyakin da ta samar zuwa kasuwa a ƙarshen watan Yuli.
Masu sharhi sun yi hasashen Dangote zai shiga cikin jerin hamshaƙan attajirai 20 na duniya
Masu sharhi sun yi hasashen cewa Dangote zai shiga cikin jerin hamshaƙan attajirai 20 na duniya, lokacin da matatar man fetur ɗin sa ta fara aiki.
Uche Madubuogu, mai sharhi kan harkokin kasuwanci kuma ma'aikacin banki, ya gayawa Legit.ng cewa matatar man Dangote za ta kai shi cikin jerin attajiran duniya 20.
Dangote Ya Bayyana Abin Da Buhari Ya Fada Masa Lokacin Da Ya Gabansa Ya Fadi
A wani rahoton na daban kuma, Aliko Dangote ya bayyana abinda shugaba Buhari, ya gaya masa lokacin da ya yi niyyar barin aikin matatar man fetur ɗinsa.
Hamshaƙin attajirin ya bayyana cewa shawarwarin da ya samu daga wajen Buhari ne suka sanya ya ci gaba da aikin.
Asali: Legit.ng