Jami'an DSS Sun Mamaye Ofishin EFCC Na Legas, Sun Hana Jami’an Shiga Ofis

Jami'an DSS Sun Mamaye Ofishin EFCC Na Legas, Sun Hana Jami’an Shiga Ofis

  • Da safiyar ranar Talata, 30 ga watan Mayu ne aka bayyana cewa jami'an tsaro na farin kaya (DSS) sun mamaye ofishin hukumar EFCC da ke Legas
  • Jami'an na farin kaya sun kuma hana dukkanin wasu jami'ai na hukumar ta EFCC shiga ofishin nasu
  • An bayyana cewa tuntuni akwai takun saƙa a tsakanin hukumomin guda biyu kan batun mallakar ginin ofishin

Lagos - Rahotanni da muka samu sun bayyana cewa jami'an hukumar tsaro na farin kaya (DSS), sun hana jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) shiga ofishinsu da ke Ikoyi, jihar Legas.

Wata majiya da ba a bayyana sunanta ba ta shaidawa jaridar Premium Times cewa, jami’an tsaron na farin kaya DSS sun toshe ginin baki ɗaya tare da ajiye tankar yaƙi mai sulke a gabansa.

Kara karanta wannan

Matakalar Taron Rantsar da Abba Gida Gida Ta Rushe Yayin Bikin Rantsar da Shi a Kano

Jami'an DSS sun mamaye ofishin EFCC na Legas
Jami'an DSS sun hana jami'an EFCC shiga ofis a Legas. Hoto: The Cable
Asali: UGC

DSS sun aje tankar yaƙi gaban ofishin

Majiyar ta ƙara da cewa jami'an na DSS sun zo da tankar yaƙi domin tsorata jami'an na hukumar ta EFCC ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai dama an ce a cikin 'yan kwanakin nan akwai takun-saƙa tsakanin jami'an na hukumar jami'an farin kaya da na EFCC kan batun mallakar ginin, Punch ta yi rahoto.

Har ya zuwa lokacin da ake wannan rahoto, jami’an na DSS sun hana dukkan wani jami’in EFCC da ke ofishin da ke titin Awolowo, Ikoyi shiga wurin.

Gwamnan Benue ya yi martani kan batun gayyatar EFCC

A baya, kun ji cewa gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya fito yana faɗin cewa a shirye yake ya amsar gayyatar EFCC da ma sauran hukumomin da ke yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan wani rahoto da aka wallafa, inda a ciki aka bayyana cewa gwamnan na wasan ɓuya da hukumar ta EFCC.

Kara karanta wannan

To Fa: Gwamnan Arewa Na PDP Ya Magantu Kan Yuwuwar Ya Koma Jam'iyyar APC

Gwamnoni 28 da EFCC za ta bincika

A wani labarin mu na can baya, mun kawo muku cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta sanar da cewa za ta binciki gwamnoni 28 da suka kammala wa'adinsu a ranar 29 ga watan Mayu.

Sai dai daga cikinsu akwai waɗanda sun sake yin nasarar lashe zaɓe, wanda hakan ya basu damar komawa kujerarsu karo na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng