Tawagar Biden Ta Iso Najeriya Don Rantsar da Sabon Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu
- Daga karshe dai ranar rantsar da Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasan Najeriya ta iso
- Abin ban sha’awa, gwamnatin kasar Amurka ta turo wakilai domin halartar wannan taro mai muhimmanci a Najeriya
- Tawagar da Joe Biden ya turo yanzu haka ta iso Najeriya a ranar Lahadi 28 ga watan Mayu, ta samu tarba
FCT, Abuja - Kwamitin mutum tara da gwamnatin Joe Biden na Amurka ta turo zuwa Najeriya ya iso domin halartar bikin rantsar da Bola Ahmad Tinubu.
Tawagar ta samu tarba a Najeriya ne a ranar Lahadi 28 ga watan Mayu a ofishin jakadancin Amurka a Najeriya.
Yadda tawagar Amurka ta iso Najeriya a ranar Lahadi
A wani sakon da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya yada a kafar Twitter, wanda wakilinmu ya gani, an tabbatar da isowar wakilan shugaban kasa Joe Biden.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar ta ofishin jakadancin:
“Barkanku da zuwa Najeriya! Muna farin cikin karbar wakilai da @POTUS Biden, karkashin jagorancin @SecFudge daga sashen gidaje da ci gaban birni a lokacin da suka gamu damu a Abuja don halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.”
Cece-kuce game da sakamakon zabe, wasu basu amince a rantsar da Tinubu ba
Idan baku manta ba, ‘yan Najeriya sun shirya tsaf domin ganin yadda za a rantsar da Bola Ahmad Tinubu a gobe Litinin.
Duk da haka, akwai masu bayyana cece-kuce kan yadda za a rantsar da sabon shugaban duk da kuwa kararrakin da ke gaban kotu game da sakamakon zaben shugaban kasa na bana.
Wannan yasa, Fasto Tunde Bakare ya bayyana cewa, ba zai taba kiran Bola Tinubu ba a matsayin shugaban kasa saboda bai gamsu da sakamakon zaben na 25 ga wtaan Faburairu ba.
Idan Tinubu ya bani minista zan karba, inji Tunde Bakare
A wani labarin na daban, Tunde Bakare ya ce zai iya karbar kujerar minista daga hannun Bola Tinubu duk da kasancewarsa mai adawa da sakamakon zaben shugaban kasa.
Ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da bayyana shirin yadda za a rantsar da Tinubun a farkon mako mai zuwa.
A cewar Bakare, bai damu ba, idan dai dan Najeriya zai amfana, tabbas zai karbi kujerar minista a mulkin Tinubu.
Asali: Legit.ng