Abin da Zan Yi Idan Tinubu Ya Ba Ni Matsayin Minista, Fasto Tunde Bakare Ya Magantu

Abin da Zan Yi Idan Tinubu Ya Ba Ni Matsayin Minista, Fasto Tunde Bakare Ya Magantu

  • Daya daga cikin fastocin da ke sukar zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana matsayarsa ga mulkin Tinubu
  • Tunde Bakare ya ce, idan Tinubu zai ba shi minista zai karba, amma zai gidaya sharudda kafin ya karba
  • A baya, Tunde ya ce ba zai amince ya kira Bola Ahmad Tinubu shugaban kasar Najeriya ba saboda dalilai

Najeriya - Fasto Tunde Bakare, babban limamin Cocin Citadel Global Community, ya ce zai karbi kujera hannu bibbiyu idan gwamnatin zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ta ba shi mukamin minista.

Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga tambayar da aka yi masa a wata tattaunawar yanar gizo a ranar Asabar, 27 ga watan Mayu, Legit.ng ta tattaro.

Fasto Bakare ya ce idan aka kira shi aka ba shi minista a gwamnatin Tinubu mai jiran gado, zai karba amma da sharudda.

Kara karanta wannan

"Ka Soke Kujerar Karamin Minista": Shugabannin Addinai Sun Jero Abubuwan Da Suke So Tinubu Ya Yi Da Zaran Ya Karbi Mulki

Bakare ya ce zai karbi minista idan Tinubu ya ba shi
Malamin coci Tunde Bakare | Hoto: Pastor Tunde Bakare
Asali: Facebook

Zan karbi minista daga hannun Tinubu, inji Bakare

Jaridar The Punch ta ruwaito shi yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Duk ba ni da burin zama minista, ko kadan, a baya an yi min tayin hakan amma na ki, rayuwata ban dauke ta kawai don daukar hotuna da shugaban kasa ba da kuma yin musafaha.
"Amma za mu yi idan har dan kasa daya zai amfana da hakan."

Tun bayan fara neman shugabancin Tinubu, Bakare na daga cikin wadanda ke sukar zababben shugaban kasar saboda zaban abokin takara Musulmi a madadin Kirista.

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya, yayin da Muhammadu Buhari zai bar kujerar a ranar.

Ba Zan Taba Kiran Tinubu Shugaban Kasata Ba, inji Fasto Tunde Bakare

A bangare guda, Bakare ya ce ba zai taba kiran Bola Tinubu a matsayin shugaban kasan Najeriya ba saboda bai gamsu da kasancewarsa shugaban kasar ba.

Kara karanta wannan

Jawabin Ban Kwana: Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

Bakare ya fadi hakan ne tare da cewa, yana zargin an yi magudi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a Najeriya a ranar 25 ga watan Faburairun da ya gabata.

Tun farko, Bakare dai na daya daga cikin masu adawa da tsarin Bola Ahmad Tinubu da ma jam'iyyar APC baki daga saboda dalili na addini da ya gindaya a tsakani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.