Buhari Ya Kaddamar Da Katafaren Gidan Gyaran Hali Mai Daukan Fursunoni 3,000 A Kano

Buhari Ya Kaddamar Da Katafaren Gidan Gyaran Hali Mai Daukan Fursunoni 3,000 A Kano

  • Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa saboda a rage cunkoso kuma domin bai wa fursunoni kula ya sa gwamnatinsa ta gina gidajen gyaran hali na zamani
  • Buhari ya bayyana hakan ne a wajen bikin ƙaddamar da sabon gidan gyaran hali da ya gina na Janguza da ke Kano
  • Ya kuma ce sabon gidan zai rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen jigilar fursunoni zuwa kotu, sakamakon kotun tafi da gidanka da aka gina a ciki

Jihar Kano - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a, ya ƙaddamar wani katafaren gidan gyaran hali na zamani mai cin mutane 3,000 a Janguza, jihar Kano.

Shugaban wanda ya ƙaddamar da gidan ta kafar sadarwa, ya ce gwamnatinsa ta gina irin gidan gyaran halin na zamani a kowace daga cikin shiyyoyi shida da muke da su a ƙasar nan, kamar yadda ya zo a rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Shekaru 8 Na Shafe Ina Ceto Yara ’Yan Najeriya Daga Hannun ’Yan Bindiga, Inji Buhari

Buhari ya kaddamar da gidan gyaran hali na janguza Kano
Buhari ya ce saboda rage cunkoso suka gina sabon gidan gyaran hali na Kano. Hoto: PR Nigeria
Asali: UGC

Domin rage cunkoso aka gina gidajen

Ya kuma ce dalilin gina su shi ne don rage cunkoso da ake samu a gidajen gyaran halin da suke a sassa daban-daban na ƙasar nan, ta yadda suma fursunonin za su samu kula ta musamman.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sanarwar da kakakin hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya (NCoS), Abubakar Umar ya fitar, Buhari ya ƙara da cewa sabon ginin zai rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen jigilar fursunonin zuwa kotuna, domin ginin yana da ɗakunan kotu har guda biyar domin aiwatar da shari'o'i cikin gaggawa.

A nasa jawabin, Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbeshola, ya yi kira ga gwamnatocin jihohin ƙasar nan da su ɗauki nauyin ciyar da fursunoninsu na jihohi da ke tsare a gidajen yarin gwamnatin tarayya.

Yace hakan ya yi dai-dai da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da aka yi wa kwaskwarima.

Kara karanta wannan

May 29: “Buhari Ya Gaza, Dole a Fada Masa”, Inji Gwamnan Arewa

An nemi al'umma da su daina tsangwamar waɗanda suka je gidan gyaran hali

Da yake jawabi a madadin Gwamnan jihar Kano, sakataren gwamnatin jihar ta Kano Alh. Usman Alhaji, ya bayyana fatansa cewa, sabon gidan zai inganta ayyukan hukumar gidajen gyaran halin.

A jawabinsa na godiya, shugaban hukumar gidajen gyaran hali na ƙasa Halliru Nababa, ya yi kira ga al'umma da su daina tsangwamar waɗanda suka je gidajen gyaran hali.

Nababa ya ce tsangwamar wadanda suka dawo daga gidajen gyaran halin na iya maida su zuwa inda suka fito, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Buhari ya bayyana dalilin da ya sa bai riƙa sanyawa majalisa baki ba

A wani labarin namu na baya, shugaban ƙasa mai barin gado Muhammadu Buhari, ya bayyana dalilin da ya sa bai riƙa tsoma baki ba a tsawon shekaru takwas da ya yi ya na mulki cikin harkokin majalisar ƙasar nan.

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake ƙaddamar da sabon ginin cibiyar nazarin majalisu da dimokuraɗiyya ta ƙasa a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng