Shekaru 8 Na Shafe Ina Ceto Yara ’Yan Najeriya Daga Hannun ’Yan Bindiga, Inji Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin ci gaba da ceto yaran da ke hannun ‘yan bindiga a Najeriya
- Da fari, shugaban ya ce gwamnatinsa shekaru takwas ta yi tana ceto yara da hannun ‘yan bindiga a bangarori daban-daban
- Idan baku manta ba, saura kwanaki kadan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a mulkin da ya shekara takwas yana yi
FCT, Abuja - Yayin da gwamnatinsa ke kan ganiyar karewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kadan daga kokarin da ya dukufa yana yi tsawon shekaru.
A cewar Buhari, gwamnatinsa ta shafe shekaru takwas cif-cif tana yunkurin ceto yaran da tsageru suka sace daga hannun ‘yan bindiga.
Ya kuma ce, gwamnatin ta yi hakan ne a bangarori daban-daban na kasar da ke yawan fama da farmakin ‘yan ta’adda.
Yaushe Buhari ya yi wannan batu?
Shugaban ya fito ya yi wannan bayanin ne a ranar Asabar 27 ga watan Mayu a cikin sakonsa na bikin Ranar Yara ta Duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa, yana takaici da kuma jin “radadin da iyaye ke ji” bisa yadda rashin tsaro ya dabaibaiye ‘yan Najeriya, musamman yadda ake garkuwa da dalibai a makarantun kasar.
A cewar sakon na Twitter da Buhari ya yada:
"Kuma ina jin radadi na rashi, da zakuwa, da bacin rai da matsalar tsaro ta jawo, wacce muka yi aiki tukuru akai don shawo kanta tsawon shekara takwas."
Har ila yau, Buhari ya kuma yi tsokaci ga yadda gwamnatin nasa ke aiki tukuru don ganin an ceto yara da kuma tabbatar da tattaunawa ta ceto yaran.
Ya kara da cewa:
"Cikin shekara takwas, mun mayar da hankali kan yara wajen tattaunawa da kuma yunkurin ceto da yawa daga cikinsu bayan an yi garkuwa da su, kuma muka ci gaba da neman inda sauran suke."
Daga karshe, shugaban ya ce yana da yakinin za a ci gaba da ceto sauran wadanda ke hannun ‘yan ta’addan nan ba da jimawa ba.
Buhari ya gaza, inji gwamnan PDP Ortom
A wani labarin, kunji yadda gwamnan PDP a jihar Benue ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya yi hakan ne daidai lokacin da ya saura kwanaki kadan shugaban kasar ya sauka daga mulkin Najeriya.
A cewar Ortom, shugaban kasa ya gaza, don haka dole a fada masa gaskiyar yadada ya ba ‘yan Najeriya kunya.
Asali: Legit.ng