Yadda Masu Kwacen Waya Suka Shiga Anguwanni 2, Suka Kashe Mutane a Kano
- Tawagar 'yan daba da ake zargin masu kwacen waya ne sun halaka aƙalla mutum 6 a Unguwannin cikin birnin Kano
- Wasu da abun ya faru a kan idonsu, sun ce da yawan waɗanda miyagun suka kashe sun dawo ne daga Masallaci Sallar Asuba
- Kakakin yan sanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce a halin yanzun suna kan bincike
Kano - Aƙalla mutum 6 suka rasa rayuwarsu yayin da wasu miyagun 'yan daba da ake zaton masu kwacen waya ne suka farmaki mutanen Unguwar Kabara da Gwangwazo, cikin birnin Kano.
Daily Trust ta tattato cewa lamarin ya faru da sanyin safiyar ranar Jumu'a kuma ya ɗaga hankulan mazauna Unguwamnin. An ce masu ƙwacen sun riƙa caka wa duk wanda suka gani wuƙa.
Ganau sun bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da tsagerun suka kashe ba su ma san meke faruwa ba, domin ma fi yawansu sun dawo ne daga Masallaci sallar Asuba.
Canja Fasalin Naira: An Faɗi Matakan da Ya Kamata Tinubu Ya Ɗauka Kan Gwamnan CBN da Wasu Jiga-Jigai
Ɗaya daga cikin mutanen Unguwannin da lamarin ya faru, Aminu Auwal, ya ce bisa dole ya ruga da gudu domin tsira da rayuwarsa amma yana kallo suka kashe maƙocinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Auwal ya ce:
"Mamana ta aike ni na ɗebo ruwa, ina tsaye na hangi maƙocin gidanmu yana gudu kuma yana kururuwan neman taimako, lokacin sun biyo shi."
"Suka kama shi a kusa da inda nake tsaye, nan take suka daɓa masa wuka har lahira, dole na sa kafa na gudu idan ba haka su haɗa da ni. Ina tantamar a ce masu kwacen waya ne."
Fatima Mukhtar, babbar yayar ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe a harin, ta ce 'yan daban sun kama ƙaninta, suka masa yankar rago, sannan suka kwace wayarsa.
Ta ce
"Yanzu muka samu labarin 'yan daba sun yanka shi, bamu san wane laifi ya musu ba. Banda shi sun kashe wasu mutum uku a wurin, duk tare aka musu jana'iza."
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce a halin yanzun jami'an yan sanda na kan bincike game da lamarin.
Wani mazaunin cikin garin Kano kuma malamin makaranta, Sanusi Isiyaku, ya tabbatarwa Legit.ng Hausa faruwar lamarin, ya ce lamarin na ƙara yawaita a cikin birni.
Isiyaku, mamban jam'iyyar NNPP ya ce a saninsa mutane 8 suka rasa rayuwarsu a hannun masu kwacen waya ranar Jumma'a da sanyin safiya bayan sallar Subahi.
A cewarsa:
"Eh tabbas lamarin ya faru a Unguwannin Kabara, Mandawari da kuma Sagagi, a yadda na samu labarin mutum 8 aka kashe. A zahirin gaskiya batun masu kwacen waya ya yi yawa."
"A yanzu akwai Unguwannin da ba'a dare, idan ka bi da daddare akwai matsala, wannan na ɗaya daga cikin abinda muke fatan sabon gwamna zai koƙarin magance mana."
Gwamnatin Kano Ta Wanke Doguwa
A wani rahoton na daban kuma kun ji cewa Gwamnatin Kano ta wanke Ɗan majalisar tarayya, Doguwa, daga zargin kisan kai.
Kwamishinan shari'a na jihar Kano, Lawan Musa Abdullahi ya ce binciken da suka gudanar ya nuna ba a sami Doguwa da laifi ba.
Asali: Legit.ng