Diezani Ta Kai Karar Hukumar EFCC Gaban Kotu Bisa Zargin Bata Mata Suna

Diezani Ta Kai Karar Hukumar EFCC Gaban Kotu Bisa Zargin Bata Mata Suna

  • Tsohuwar ministan man fetur, a gwamnatin Goodluck Jonathan, Diezani Alison-Madueke ta kai ƙarar hukumar EFCC gaban kotu
  • Diezani ta kuma haɗa da Antoni janar na gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, a cikin ƙarar da ta shigar gaban kotu
  • Tsohuwar ministar tana neman da su biya ta diyyar N1bn bisa ɓata mata suna da tozarcin da suka yi a idon duniya

Abuja - Tsohuwar ministar man fetur a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, Diezani Alison-Madueke, ta maka hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC da Antoni janar na tarayya a gaban kotu.

Aminiya tace Diezani ta shigar da ƙara a kotun ne inda ta ke buƙatar hukumar EFCC da Abubakar Malami, su biya ta diyyar N1bn saboda ɓata mata suna.

Diezani ta maka EFCC kara gaban kotu
Diezani na neman a biya ta diyyar N1bn Hoto: Thenation.com
Asali: UGC

A cikin ƙarar wacce lauyan Diezani, Mike Ozekhome (SAN) ya shigar, ta kuma buƙaci kotun ta tilasta wa EFCC ta wallafa mata saƙon ban-haƙuri a cikin aƙalla manyan jaridu guda uku na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Ta Nemi Dakatar da Rantsar da Bola Tinubu

Tsohuwar Ministar ta kuma ce dole jaridun su haɗa da Thisday, The Punch da kuma The Sun, kuma a aiwatar da wallafar a cikin kwana bakwai da yanke hukuncin kotun, cewar rahoton Tribune.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Diezani ta zargi hukumar EFCC da ɓata mata suna

Ta ce wallafe-wallafen da EFCC ta yi a kanta, ta yi su ne da nufin ganin ta ɓata mata suna da tozarta ta da cin zarafinta tare da mayar da ita abar dariya a idon duniya.

Ta ce babban dalilinta na shigar da ƙarar shine kan wasu, kan wasu sarƙoki da kayan kwalliya da suka kai na Dalar Amurka $40m, waɗanda aka ce mallakinta ne, saboda babu wata kwakkwarar hujja da ta nuna cewa mallakinta ne har zuwa lokacin da aka ƙwace su bayan umarnin kotu.

Ta kuma ce a ƙarshen wa’adin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ta kamu da cutar sankarar mama, inda aka garzaya da ita ƙasar Ingila don ganin likita a ranar 22 ga watan mayun 2015, sannan tun a wannan lokacin likitoci ke ci gaba da duba lafiyarta a Ingila.

Kara karanta wannan

Kotun Koli a Najeriya Ta Yanke Hukunci Kan Karar da PDP Ta Nemi a Soke Takarar Tinubu da Shettima

EFCC Ta Ƙaddamar Da Bincike Kan Gwamnoni 28 Da Mataimakansu

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasa (EFCC), ta fara ƙaddamar da bincike kan gwamnoni 28 na ƙasar nan.

Hukumat za ta haɗa da mataimakan gwamnonin a binciken da za ta yi wa gwamnonin masu barin gado, a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel