Tsohon Sojan Amurka Ya Shiga Hannu Kan Zargin Shigo da Makamai Najeriya
- An gurfanar da wani dan kasar Amurka, Donn Perkins bisa zargin shigo da makamai kasar Najeriya
- Perkins wanda tsohon sojan ruwan Amurka ne, an gurfanar da shi a gaban babbar kotun tarayya
- An yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu a kotun tarayya da ke jihar Lagos
Jihar Lagos - Mai shari’a Abimbola Awogboro na babbar kotun tarayya da ke Lagos ta tasa keyar wani dan Amurka mai suna Donn Perkins a gidan gyaran hali na Ikoyi bisa zargin shigo da makamai Najeriya.
Perkins wanda ya ce shi tsohon sojan ruwan Amurka ne, an gurfanar da shi ne a gaban kotun wanda hukumar shige da fice na kasar ta shigar bisa zargin aikata laifuka guda hudu.
Hukuncin wanda aka yanke a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu, an kama wanda ake zargin ne a watan Faburairu a tsibirin Tin-can a Apapa da ke jihar Lagos, cewar jaridar Leadership.
Mai gabatar da kara ta fadi laifukansa
Mai gabatar da kara, Mrs Bode-Ayeni ta fadawa kotu cewar an kama dan Amurkan ne saboda ya shigo da muggan makamai ba ta hanyar da ya dace ba, cikin makaman akwai AK-47 fiye da 30 sai kuma harsasai da dama da sauran muggan makamai a tare da shi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ta kara da cewa wanda ake zargin ya boye makamai a cikin kwantaina da ya yi kokarin shigo da su kasar Najeriya ta tsibirin Tin-can a Lagos, ta ce hakan ya sabawa dokokin Najeriya wanda ya ke dauke hukunci mai tsanani.
Perkins ya musanta zargin da ake tuhumarsa akai
Wanda ake zargin ya musanta zargin da ake masa, a dalilin haka, mai gabatar da kara ta roki kotun da ta sake saka rana don ci gaba da sauraran karar da kuma ajiye shi a gidan yari har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Yayin da lauyan wanda ake zargi, Blessing Jaiyeola ta roki korun da ta ajiye Perkins a wurin masu korafe-korafe har zuwa lokacin ci gaba da sauraran karar, cewar rahotanni.
Mai shari’a, Awogboro bayan sauraran korafe-korafe daga kowane bangare, ta umarci da a ajiye wanda ake zargin a gidan gyaran hali kuma ta dage sauraran karar har zuwa 6 ga watan Yuni don ci gaba da sauraran karar.
Amurka ta Kakaba Wa 'Yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga Cikinta Saboda Raina Dimokradiyya
A wani labarin, hukumomi a kasar Amurka sun ce za su kakaba wa 'yan Najeriya takunkumin hana shiga kasar bisa zargin yi wa dimukradiya karan tsaye.
Sakataren gwamnatin kasar, Anthony Blinken ne ya bayyana haka a ranar 15 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng