Daga Karshe, Jirgin Saman Najeriya Ya Sauka a Birnin Tarayya Abuja

Daga Karshe, Jirgin Saman Najeriya Ya Sauka a Birnin Tarayya Abuja

  • Daga karshe bayan dogon lokaci da jinkirin da aka samu, Jirgin saman Najeriya ya sauka a birnin tarayya Abuja
  • Gwamnatin tarayya ta sha alwashin cewa Nigeria Air zai fara aiki gadan-gadan gabanin shugaba Buhari ya sauka a mulki
  • Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya ce bayan dogon lokaci da gargadar da aka samu, da taimakon Allah jirgi ya dira a Najeriya

Abuja - Jirgin sama mallakin 'Nigeria Air' ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe a birnin tarayya Abuja yau Jumu'a 26 ga watan Mayu, 2023.

Daily Trust ta rahoto cewa a ɗazun, Jirgin saman wanda ya taso daga Addis Ababa, ƙasar Ethiopia, ya gama shirin lulawa sararin samaniya zuwa gida Najeriya.

Nigeria Air.
Daga Karshe, Jirgin Saman Najeriya Ya Sauka a Birnin Tarayya Abuja Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wata majiya ta shaida wa wakilin jaridar cewa jirgin saman, wanda tuni aka masa fenti da kalolin Najeriya, ya gama shirin kamo hanya zuwa Abuja daga filin jirgin Ethiopia.

Kara karanta wannan

Daga Wurin Taron Miƙa Mulki, Shugaba Buhari Ya Faɗi Jihar da Jirginsa Zai Fara Sauka Kafin Tafiya Daura

Bidiyon lokacin da jirgin saman ya sauka a Abuja

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

FG ta tabbatar da isowar jirgin

Ministan sufurin jiragen sama na tarayyan Najeriya, Hadi Sirika, ya tabbatar da isowar jirgin saman a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Jumu'a.

Ya ce:

"Allah ya kawo mu, dukkan godiya ta tabbata ga Allah mai girma da ɗaukaka. An ɗauki dogon lokaci, hanya ba daɗi, gargada da faɗi tashi, muna ƙara gode wa waɗanda suka mara mana baya."
"Wannan abu ba yin mu bane, iko ne na Allah, zai amfane mu da sauran 'ya'ya da jikokinmu masu tasowa nan gaba. Ina rokon Allah ya sa ya amfani ƙasar mu da al'umma baki ɗaya."

Channels tv ta rahoto cewa wannan ci gaban wani ɓangare ne na fara aikin jirgin saman Najeriya bayan tsawon lokaci ana ta cece-kuce da jinkiri.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Gwamnatin Buhari Ta Ayyana Hutun Kwana 1 Saboda Bikin Rantsar da Tinubu

A watan Maris, Hadi Sirika, ya ce jirgin zai fara aiki a Najeriya gabanin ƙarewar wa'adin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a watan Mayu.

Daga Wurin Mika Mulki Zan Wuce Kaduna Kafin Tafiya Daura, Shugaba Buhari

A wani rahoton na daban Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana miƙa mulki, tun daga wurin zai hau jirgi zuwa gidansa na jihar Kaduna.

Shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari ya ce daga filin bikin miƙa mulki zai hau jirgi zuwa gidansa na Kaduna.

Ya ce a kowace rana sai ya ƙidaya ragowar kwanakin da suka rage masa saboda ya ƙosa ya sauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel