An Kama Mabarata 50 Da Yara Masu Talla A Tituna A Shahararriyar Jihar Kudu
- Gwamantin jihar Anambra ta kama mutane fiye da 50 a titunan birnin Awka don rage cinkoso a titunan birnin
- Hukumar tsafta da kiyaye lafiya ta jihar ce ta kaddamar da wannan samame don rage barace-barace a jihar
- Hukumar ta koka kan yadda abin ke karuwa a birnin musamman yara da ke talla ba tare da zuwa makaranta ba
Jihar Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta kama akalla mabarata 50 da yara masu tallace-tallace a manyan tituna don rage yawan cinkoso da kazanta a jihar.
Hukumar Tsafta da Kiyaye Lafiya ta Anambra (OCHA) karkashin ma’aikatar mata da jin dadin jama’a ita ta kaddamar da wannan ran gadi a babban birnin jihar, Awka da yankunan da kewaye da ita.
Daily Trust ta tattaro cewa an kaddamar da wannan kame ne don rage yawan cinkoso da kazanta a birnin da kuma ceto yaran da ba sa zuwa makaranta daga kan tituna don cimma muradun gwamnatin jihar.
Samamen an kaddamar da shi ne a kwanan Arroma da Akwata da Regina Ceali, sai kuma bayan gari ta Amawbia da kasuwar Eke da ke Awka da sauran wurare daban-daban.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daga cikin wadanda aka kama akwai maza da mata da kuma yara kanana wadanda suka fito daga bangare daban-daban na kasar Najeriya, cewar rahotanni.
Kwamishinan mata da walwalan jama'a ta magantu akan lamarin
Kwamishinan mata da jin dadin al’umma, Mrs Ify Obinabo ta bayyana cewa ana samun yawan tallace-tallace na yara kanana da suke yawo a titunan birnin da yankunan da suke kusa don hana yawan saba dokar da take kare hakkin yara da gwamnatin jihar ta dauru akai.
Ta kara da cewa gwamnatin jihar ta nuna rashin jin dadinta akan aikatau na yara kanana musamman tare da hana su hakkinsu na zuwa makaranta.
Ta ce duk wasu yara kanana da aka gani akan tituna suna tallace-tallace musamman a lokacin makaranta, za a kamasu kuma a kai su zuwa makaranta.
Mabaratan sun koka kan kuncin rayuwa
Mafi yawa daga cikin mabaratan sun bayyana cewa kuncin rayuwa ne ya jefa su cikin wannan bara da kuma rashin samun taimakon kudi.
A karshe sun roki da a taimaka musu da kudi don samun jarin da za su dogara da kansu su kuma saka yaransu a makaranta.
Yan Sanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Harin Jami'an Amurka a Jihar Anambra
A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta yi nasarar cafke wasu da ake zargi da kai hari kan jami'an Amurka.
A yayin harin hukumomi sun tabbatar da cewa an kashe mutane bakwai a karamar hukumar Ogbaru ta jihar.
Asali: Legit.ng