Kotu Ta Daure Usman A Gidan Yari Kan Satar 'Bible' 4 Da Kudade

Kotu Ta Daure Usman A Gidan Yari Kan Satar 'Bible' 4 Da Kudade

  • Kotu da ke zamanta a Kabusa cikin Abuja ta daure wani da ake zargi da sace Injila guda hudu da wasu takardu
  • Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar 25 ga watan Mayu, inda ake zarginsa da sata da kuma wuce gona da iri
  • Mai shari’a, Mallam Abubakar Sadik ya ba da umarnin daure wanda ake zargin bayan amsa dukkan laifukansa

FCT, Abuja - Wata kotu da ke zamanta a Kabusa da ke birnin Abuja a Najeriya ta daure wani mai suna Zakaraya Usman watanni biyu a gidan yari bisa zargin satar Injila guda hudu.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu, inda ake zarginsa da sata.

Kotu a Najeriya
Kotu Ta Daure Wani Watanni 2 a Gidan Kaso Saboda Satar Linjila. Hoto: Daily Post
Asali: Twitter

Wanda ake zargin mai shekaru 30 bayan satar Linjilan, ya kuma saci wadansu takardun cikewa na majami’ar ga sabbin mambobi.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Wanke Doguwa Daga Zargin Kisan Kai

Mai shari’a, Malam Abubakar Sadik ya umarci daure wanda ake zargin bayan ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa akansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sadik ya kuma ba shi daman biyan kudi kimanin N10,000 ko kuma zuwa gidan gyaran hali, cewar Punch.

“Bisa ga amsa laifukan da ake tuhumar ka akai, don haka an yanke maka hukuncin watanni biyu a gidan yari ko kuma biyan N10,000."

Mai shari'a ya gargadi wanda ake zargin

Mai shari’ar ya shawarci wanda ake zargin da kada ya maimaita wani mummunan hali, yayin da gargade shi da cewa kotu ba za ta sassauta masa ba idan har ya kuma aikata hakan.

Tun farko, mai gabatar da kara, Mista O.S Osho ya fada wa kotu cewar shugaban masu tsaron majami’ar Mista David Usman ya kai rahoton abin da ya faru a ofishin ‘yan sanda na Durumi.

Kara karanta wannan

Hukumar NSCDC Ta Cafke Masu Kwacen Wayoyi 5 a Kano, Ta Farautar Masu Siyan Wayoyin

An bayyana yadda lamarin ya faru

Osho ya ce wanda ake zargin ya tsallaka mashigar majami’ar da kuma sace kananan Linjila guda uku da babba guda daya, sannan lemon kwalba na ‘Caprisonne’ guda 14 da takardun shaida guda 14 da kuma wasu takardun da sabbin mambobi ke cika wa a majami’ar.

Sauran kayan sun hada da rigar masu gadi da wasu riguna guda biyu da jaka da kuma kudi, cewar rahotanni.

Mai gabatar da karan ya ce dukkan wadannan abubuwa a yayin binciken ‘yan sanda an same su a wurinsa.

Kotu Ta Raba Auren Fasto Saboda Jibgar Matarsa, An Mallaka Wa Matar Kadarorinsa

A wani labarin, Kotu da ke zamanta a jihar Edo ta datse auren Fasto saboda yawan dukan matarsa.

Faston mai suna Oni Muyiwa ma'aikacin jinya ne wanda ya saba sakin mata da son auren jari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.