'Ƴan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kan Jami'an 'Yan Sanda a Jihar Ebonyi, Sun Halaka Uku Daga Ciki
- Miyagun ƴan bindiga ɗauke ɗa makamai sun sake kai mummunan farmaki kan jami'an ƴan sanda a jihar Ebonyi
- Ƴan bindigan sun halaka jami'an ƴan sanda mutum uku suna tsaka da aikinsu na duba ababen hawa, a yayin harin
- Rundunar ƴan sandan jihar ta fita farautar miyagun ƴan bindigan inda jami'anta suka halaka wasu daga cikinsu da kwato makamai
Jihar Ebonyi - Ƴan bindiga sun sake halaka jami'an ƴan sanda uku a jihar Ebonyi, da ke a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa, lamarin ya auku ne a ranar Laraba da safe a ƙauyen Oshiri, cikin ƙaramar hukumar Onicha ta jihar.
Kakakin ƴan sandan jihar, Onome Onovwakpoyeya, ita ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar da yammacin ranar Laraba.
Ms Onovwakpoyeya, ta bayyana cewa ƴan bindigan sun farmaki jami'an ƴan sandan ne lokacin da su ke aikin duba ababen hawa a ofishin ƴan sanda na Oshiri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Abin takaici ƴan sanda uku sun rasa rayukansu. Ɗaya ya samu raunika inda ake duba lafiyarsa yanzu haka a asibiti." A cewarta.
Ƴan sanda sun fita farautar ƴan bindigan
Kakakin rundunar ƴan sandan ta kuma bayyana cewa, jim kaɗan bayan harin, an tura ƙwararrun jami'an ƴan sanda zuwa yankin domin farauto ƴan bindigan.
"An halaka mutum biyu daga cikin miyagun ƴan bindigan sannan wasu da dama suka gudu ɗauke da raunikan harbin bindiga a tare da su." A cewarta.
Onome ta kuma bayyana cewa jami'an ƴan sandan sun kwato kayayyaki da makamai da dama a hannun ƴan bindigan, cewar rahoton The Nation.
Daga cikin abubuwan da aka kwato sun haɗa da mota guda ɗaya ƙirar Lexus ES-350, bindiga ƙirar AK-47, harsasai da sauran makamai masu yawa.
An kuma ƙwato miyagun ƙwayoyi, layoyi, gangunan tsafi daga hannun ƴan bindigan.
'Yan Bindiga Sun Halaka Sufetan 'Yan Sanda a Ebonyi
A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa miyagun ƴan bindiga sun halaka wani sufetan ƴan sanda a jihar Ebonyi.
Ƴan bindiga sun kuma raunata wasu jami'an ƴan sanda biyu, a mummunan harin da suka kai musu a wajen shingen binciken su.
Asali: Legit.ng