A Taron FEC Na Karshe, Buhari Ya Amince Gwamnatinsa Ta Kai Ayyuka Zuwa Daura

A Taron FEC Na Karshe, Buhari Ya Amince Gwamnatinsa Ta Kai Ayyuka Zuwa Daura

  • Ministan harkokin wutar lantarki ya ce FEC ta amince da wasu kwangiloli da za ayi a garurwan Najeriya
  • Abubakar Aliyu ya ce gwamnatin tarayya ta yarda ayi ayyukan wuta a jihohin Katsina, Yobe da Ogun
  • A zaman karshe da majalisar FEC tayi, an amince da wasu takardun Ministocin shari’a da harkokin mata

Abuja - A zaman da aka yi ranar Laraba, Majalisar zartarwa ta FEC ta amince da wasu kwangiloli da za su inganta karfin wutar lantarki a sassan kasar nan.

Daily Trust ta rahoto Ministan lantarki, Abubakar Aliyu ya na cewa daga cikin kwangilar da aka amince akwai daura na’urar 33 KV a Daura da ke Katsina.

Kamfanin da aka ba kwangilar shi ne Power Deal Construction Limited, aikin zai ci Naira biliyan 4.

Shugaban kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a FEC Hoto: @Buhari Sallau
Asali: Facebook

Mai girma Ministan ya ce majalisar FEC tayi na’am da kwangilar inganta lantarki a karkashin wani tsari da aka fito da shi a ofishin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kafin Buhari Ya Sauka Daga Mulki, An Samu Wanda Ya Maka Shugaban Kasa a Kotu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan katafaren aiki na daura layin wutan 330 KV da 132 kV da na 33 KV, 11 KV zai ci $581,629,355.93, ana sa ran a kammala aikin cikin watanni 36.

Baya ga haka, majalisar ta amince da kwangilar gina tashar 750 kw da za a rika samun wuta da karfin rana a hedikwatar kamfanin TCN na kasa.

An amince da wasu kwangiloli

Vanguard ta ce kamfanin da aka ba wannan aiki shi ne Proserv Energy Services Ltd a kan N1.6bn, nan da watanni shida ake sa ran a kammala komai.

Wani aikin wuta da aka amince da shi a jiyan shi ne kwangilar inganta tashar lantarkin Potiskum a jihar Yobe, an yarda a sayo turansfoma 132.

A zaman ne aka bada dama ga kamfanin VNK International Technologists ya gina layin wutar lantarki a Sapade a jihar Ogun a kan $10.2m da N3.3bn.

Kara karanta wannan

Jerin Ministocin Buhari 14 Da Aka Fi Damawa Da Su A Gwamnatin Tarayya Daga 2015 Zuwa Yanzu

Bayanin sauran Ministoci

Ministar harkokin mata, Pauline Tallen ta shaida cewa FEC ta amince da tsarin WEE da zai taimaka wajen karfafa mata, a rika damawa da su a Najeriya.

Shi kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ya ce an duba dokokin Najeriya da kasar Afrika ta Kudu la’akari da cigaba da aka samu na zamani.

Zaman karshe da Buhari

Majalisar zartarwa ta kasa tayi zaman da ya kasance na ban-kwana a jiya. Festus Keyamo da Ramatu Tijjani Aliyu sun soki tsarin rabon Ministoci.

An samu labari cewa a nan ne Ministoci su ka fito karara su ka fadawa Shugaban kasa abin da suke ganin shi ne daidai kan batun karamin Minista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng