Kafin Buhari Ya Sauka Daga Mulki, An Samu Wanda Ya Maka Shugaban Kasa a Kotu

Kafin Buhari Ya Sauka Daga Mulki, An Samu Wanda Ya Maka Shugaban Kasa a Kotu

  • Patrick Osagie Eholor ya yi karar Mai girma Muhammadu Buhari a kotu a dalilin neman aron kudi
  • ‘Dan gwagwarmayar ya na ganin bai dace a ba Gwamnati damar karbowa Najeriya bashin $800m ba
  • Wadanda za ayi shari’a da su sun hada da Ministar kudi, Ministan shari’a da ofishin kula da bashi

Delta - Wani ‘dan gwagwarmaya wanda shi ne shugaban gidauniyar One Love Foundation, OLF ya na karar Shugaba Muhammadu Buhari a kotu.

A ranar Laraba, Vanguard ta kawo rahoto cewa Cif Patrick Osagie Eholor ya kai karar shugaban kasa a babbn kotun tarayya mai zama Asaba a jihar Delta.

Patrick Osagie Eholor ya so a hana shugaba mai barin-gado karbo bashin $800m da ya yi niyya daga bankin Duniya da sauran kungiyoyin kasar waje.

Shugaban Kasa
Shugaba Muhammadu Buhari tare da Janar Lucky Irabor Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Manyan Abubuwa 7 Da Suka Faru Tsakanin 2019 da 2023 a Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wadanda suka shigar da kara a kotun tarayyar su ne One Love Family Caring da Patrick Eholor.

Rahoton ya ce wadanda za su kare kan su a shari’ar sun hada da bankin Duniya, kungiyoyin cigaban kasashen waje da kuma shugaban kasar Najeriya.

An hada da AGF da Ministar kudi

Haka zalika ana karar Babban lauyan gwamnatin tarayya, ma’aikatar kudi da cigaban tattalin arzikin Najeriya sai kuma ofishin kula da bashi na kasa.

Gidauniyar One Love Foundation da Dr Patrick Osagie Eholor su na rokon Alkalin kotu ya hana a ci bashi da hujjar ba za ayi adalci wajen rabon kudin ba.

Ministar kudi ta ce za a raba kudin da za a karbo ga mutane miliyan 50 marasa karfi, masu karar sun ce ba abin da ke gaban gwamnatin kasar nan kenan ba.

Kara karanta wannan

Minista Ya Cigaba da Korar Shugabannin Hukumomi, Ya Ce Babu Sani ko Sabo a Mulki

Masu karar sun fake da cewa sashe na 34(1)(b) na kundin tsarin mulki ya ba kowa ‘yancin zama ‘dan kasa, suka ce karbo bashin zai jefa su a kangin bauta.

Sharadin bashin shi ne za a rika biyan kudin sannu a hankali a watannin Junairu da Yuli, za a fara biyan kudin a 2027, sannan a gama a Yulin shekarar 2051.

Zuwa yanzu ba mu da masaniyar ko an tsaida lokacin da za a saurari karar Eholor da gidauniyarsa.

Buhari ya yi sallama da FEC

Rahoto ya zo cewa Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC na bankwana da Ministoci a ranar Laraba, inda aka ji ya yi kalamai masu ratsa zuciya da ban tausayi.

Buhari ya faɗawa Ministocinsa da za su bar ofis zai jira zuwansu Daura idan kauyensa bai yi musu nisa ba saboda ganin a lokacin ba shi ne shugaba ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng