An Kama Masu Garkuwa Da Yan Kungiyar Asiri 26 A Fitaciyyar Jihar Arewa

An Kama Masu Garkuwa Da Yan Kungiyar Asiri 26 A Fitaciyyar Jihar Arewa

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da yin garkuwa da mutane tare da ceto biyu daga cikin wadanda aka sace
  • A kwanakin nan ne waɗanda ake zargin suka yi awon gaba da mutane biyu a karamar hukumar Wamba da ke jihar ta Nasarawa
  • Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ramhan Nansel, ne ya bayyana hakan a garin Lafia a ranar Laraba

Nasarawa, Lafia - Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da cafke mutane 26 da ake zargi da aikata laifuka da suka shafi garkuwa da mutane da kuma ayyukan asiri a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel ne bayyana hakan a Lafia babban birnin jihar, kamar yadda Punch ta yi rahoto.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Cafke Fursunonin da Suka Tsere Daga Magarkamar Kuje Suna Aikata Wani Laifin a Adamawa

'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane a Nasarawa
'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane a Nasarawa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

'Yan sanda sun ceto mutane biyu

Ya ce sun kuma yi nasarar kuɓutar da wasu mutane biyu da aka sace kwanan nan da ake zargin masu garkuwa da mutane da yin awon gaba da su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a ranar Laraba, Nansel ya ce, ‘yan sandan sun sami bayanan sirri ne inda daga nan suka kai samame maɓoyar masu garkuwar tare da kamo su.

Wadanda ake zargi sun amsa laifinsu

Ya ƙara da cewa waɗanda ake zargi sun amsa cewa sune suke ayyukan ta'addanci a ƙauyen na Ambaka da kewaye.

A cewarsa:

“Bisa bayanan sirri da muka samu a ranar 23 ga Mayu, 2023 da misalin karfe 4 na yamma, tawagar ‘yan sandan masu zagaye da ke aiki da rundunar ‘ofareshin dawo da zaman lafiya’, sun kai samame maɓoyar masu garkuwa da mutane a ƙauyen Ambaka da ke yankin Farin Ruwa a ƙaramar hukumar Wamba ta jihar.”

Kara karanta wannan

Mutane Hudu Sun Faɗa Komar ‘Yan Sanda a Ogun Bisa Laifin Halaka Makiyayi

“Sun yi nasarar kuɓutar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su na wani ɗan lokaci, kuma sun kama wasu masu garkuwa da mutanen su biyar, sunansu: Sale Adamu, 34, Idi Halilu, 27, Abdul Sale, 20, Mallam Gambo, 48, da Goma Halilu, 20, dukkansu maza, 'yan kauyen Ambaka. Waɗanda ake zargin sun amsa cewa sune ke yin garkuwa da mutane a ƙauyen Ambaka da kewaye.”

'Yan sanda sun cafke fursunonin da suka tsere daga gidan yari

A wani labarin da muka wallafa a baya, jami'an 'yan sanda a jihar Adamawa sun yi nasarar cafke mutane biyu da suka tsere daga gidan gyaran hali na Kuje, Abuja.

Fursunoni dai da dama ne aka tabbatar da tserewarsu daga gidan gyaran halin a wani hari da 'yan bindiga suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng