'Dan Uwan Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Rasu a Hadarin Mota
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya rasa ɗaya daga cikin 'yan uwansa sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi
- A wata sanarwa da iyalan gidansu gwamnan suka fitar, sun ce Musa Sule wanda aka fi sani da Labaran ya rasu yana da shekaru 51
- Tuni dai manyan mutane da shugabanni a jihar Nasarawa suka fara aika sakon ta'aziyya ga mai girma gwamna bisa rashin ɗan uwansa
Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya rasa ɗaya daga cikin 'yan uwansa na gidansu, Musa Sule, a wani mummunan haɗarin mota da ya rutsa da shi.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa iyalan gidansu gwamnan ne suka tabbatar da haka a wata sanarwa da suka fitar ranar Litinin. Sanarwan ta ce lamarin ya faru ranar Asabar.
A sanarwan wacce Ahmed Sule ya rattaɓa wa hannu a madadin iyalan, ya ce marigayin wanda aka fi sani da suna, Labaran, ya rasu yana da shekara 51 a duniya.
Daily Trust ta rahoto Ahmed Sule na cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Iyalan gidan Alhaji Sule Bawa na baƙin cikin sanar da rasuwar ɗansu Musa, wanda aka fi sani da Labaran da safiyar ranar Asabar 20 ga watan Mayu, 2023. Labaran ya rasu yana da shekara 51."
"Haka nan ya mutu ya bar mata ɗaya da ɗansu, iyaye, 'yan uwa maza da mata daga ciki harda mai girma gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule."
"Za'a gudanar da Addu'ar uku ranar Litinin (jiya), 23 ga watan Mayu, 2023, bayan kwana uku da rasuwarsa."
Manyan mutane sun jajantawa gwamna Sule
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tun bayan aukuwar lamarin, manyan sanannun mutane suka fara jajantawa gwamna Abdullahi Sule bisa wannan rashi na ɗan uwansa.
Tsohon gwamna kuma Sanatan Nasarawa ta Kudu, Umaru Tanko Al-Makura da kakakin majalisar dokokin jihar, Honorabul Ibrahim Balarabe Abdullahi, na cikin manyan mutanen da suka yi wa gwamna ta'aziyya.
Gwamnan Gombe ya samu nasarar zama shugaban gwamnonin arewa
A wani rahoton na daban kuma kun ji cewa Gwamnan APC Ya Samu Nasarar Zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya.
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, zai gaji gwamnan Filato mai barin gado, Simon Lalong, a matsayin shugaban ƙunguyar NSGF, zai shafe shekaru huɗu.
Asali: Legit.ng