'Yan Bindiga Sun Harbe 'Yan Uwa Biyu, Sun Sace Sama Da Shanu 1,000 a Kaduna
- Wasu 'yan bindiga da ake tunanin ɓarayin shanu ne sun harbe wasu 'yan uwa su biyu a ƙauyen Azara jihar Kaduna
- 'Yan bindigar sun kuma kora sama da shanu 1,000 a wani ƙauye Bishini da ke maƙwabtaka da ƙauyen na Azara
- Mafarauta sun yi nasarar karɓo shanun da ɓarayin dajin suka sata, kamar yadda rahotanni suka bayyana
Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun harbe wasu 'yan uwan juna biyu da aka bayyana sunayensu da Halilu Shittu da Muhammadu Shittu a ƙauyen Azara da ke jihar Kaduna.
Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da shanu sama da 1,000 a kauyen Bishini da ke maƙwabtaka da ƙaramar hukumar Kachia ta jihar.
Majiyarmu ta samu labarin cewa an kuma harbe wani mutum da ba a tantance ba a yayin harin.
Wani mazaunin garin Azara mai suna Yahuza wanda Daily Trust ta tattauna shi a ranar Lahadi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe 4 na yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɓarayin sun harbe masu aikin gawayi
Ya ce ‘yan fashin bayan sun harbe ’yan uwan a gonakinsu da ke Azara a lokacin da suke aikin gawayi, sai suka tafi Bishini suka yi awon gaba da shanu sama da 1,000 bayan sun harbe wani ɗan ƙauyen.
An tuntuɓi Sarkin Hausawan Azara, Ibrahim Isah, amma bai samu amsa kiran waya ba, sai dai wani na kusa da sarkin da ya so a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai safiyar Lahadi aka iya ɗauko gawarwakin
Mutumin ya ƙara da cewa sai da safiyar ranar Lahadi ne aka samu damar ɗauko gawarwakin, gami da yi musu sallah.
A cewarsa:
“A safiyar yau Lahadi ne aka ɗauko gawarwakin ‘yan uwan biyu daga gona, kuma a yanzu da nake magana da ku ana shirin binne gawarwakinsu.”
Ya ci gaba da cewa, mafarauta sun samu nasarar kwato shanun da aka sace, kuma suna cikin daji inda suke jiran jami’an tsaro domin su miƙa musu shanun.
Shugaban ƙauyen Bishini, Zamani Dogon Yaro, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shanu sama da 1,500.
Ya ce amma cikin hukuncin Allah an ƙwato shanun, sai dai ya ce sun rasa mutum ɗaya a yayin harin. Ya kuma ce shanun na wani Alhaji Hashimu ne.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige, ya zuwa yanzu bai tabbatar da faruwar lamarin ba saboda bai amsa kiran da aka yi masa ba.
'Yan bindiga sun sha alwashin ci-gaba da kai hari
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Jami'an Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa, Sun Aiko da Sako Mai Ta Da Hankali
Idan baku manta ba, a wani labarinmu na baya mun kawo muku cewa 'yan bindiga sun yi alkawarin ci-gaba da kai hari muddun ba a biya musu bukatar su ba.
'Yan bindigar sun nemi a janye sojoji daga garin Birnin Magaji da ke jihar Zamfara mai fama da ayyukan 'yan ta'adda.
Asali: Legit.ng