‘Yan Shi’a Sun Caccaki El-Rufai Kan Batun Rushe Asibiti Da Makarantunsu

‘Yan Shi’a Sun Caccaki El-Rufai Kan Batun Rushe Asibiti Da Makarantunsu

  • 'Yan kungiyar harkar Musulunci a Najeria (IMN) sun caccaki gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai saboda rushe musu gine-gine
  • Mambobin kungiyar sun ce ba a aiko musu da wata sanarwa da ke nuni da dalilin da ya sa za a rusa musu gine-ginen na su ba
  • Sun kuma ce su 'yan kasa ne masu son bin doka da oda, amma gwamnan na neman kai su bango

Kaduna - Mambobin ƙungiyar harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wadanda aka fi sani da Shi’a, sun yi martani kan rushe musu gine-gine.

Sun yi martanin ne a lokacin da hukumar tsare-tsare da kuma raya birane ta jihar Kaduna (KASUPDA) ta rusa wasu gidaje shida daga cikin 48 na kungiyar a Kaduna ranar Lahadi, Punch ta yi rahoto.

'yan shi'a
‘Yan Shi’a Sun Caccaki El-Rufai Kan Batun Rushe Asibiti Da Makarantu. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

‘Yan kungiyar ta IMN, sun yi jawabin ne ga manema labarai a Kaduna, da yammacin ranar Lahadin da ta gabata bayan rushe gine-ginen ƙungiyar da suka haɗa da makarantu da asibitoci da wani gida daban.

Kara karanta wannan

Ba A Je Ko Ina Ba, An Fara Zargin Gwamnan APC Da Yakar Gwamna Mai Jiran Gado

Mecece KASUPDA?

KASUPDA dai a wata sanarwa da ta fitar a makon da ya gabata, ta nemi amincewar gwamnan domin aiwatar da rusau ɗin gine-gine a fadin jihar ta Kaduna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga cikin gine-ginen da abin zai shafa har da gine-gine 48 na kungiyar IMN ƙarkashin jagorancin Sheikh Ibraheem El-Zakzaky.

Da sanyin safiyar Lahadi ne hukumar ta fara aikin rusa wasu gine-ginen na mabiya Shi’a a yankunan Kawo, Rigasa, Tudun Wada da Ungwan Rimi na jihar, inda ta yi amfani da jami’an tsaro wajen fatattakar mutanen da ke cikin gine-ginen.

Rusau ɗin da ake yi ya saɓawa ƙa'ida

Daya daga cikin jagororin kungiyar, Yunusa Lawal, ya ce rusa gine-ginen nasu na miliyoyin Naira ya saɓawa ka’ida, saboda dalilin da gwamnati ta bayar shi ne cewa an haramta ƙungiyar ta IMN.

Lawal ya kuma ce, ba a aikawa da IMN wata sanarwa kan rusau ɗin ba. Haka nan ba su ma san inda ragowar gine-ginen suke ba.

Kara karanta wannan

Bangarori 7 da Ake Jiran Bola Tinubu Ya Kawo Gyara Idan Ya Gaji Muhammadu Buhari

A cewarsa:

“Ba a ba mu wata takardar sanarwa don sanin dalilin rushewar ba, ba ma mu san wurin da sauran gine-gine 42 da suke shirin rushewar suke ba.”

Yunusa ya ƙara da cewa abinda kawai suka iya sani cikin abinda aka rubuta a takardar, shine cewa ƙungiyarsu haramtacciya ce.

Sai dai ya ce su ƙungiyarsu fa ta addini ce domin haka ba za a iya dakatar da su ba.

El-Rufai na neman kaimu bango

Yunusa ya kuma ce su 'yan ƙasa ne masu bin doka, amma gwamna El-Rufai na neman kaisu bango, ya ce dole ne su tanka a kan hakan.

Sannan kuma ya yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki kan su takawa El-Rufai birki, saboda a cewarsa za a iya samun ɓallewar rikicin da ka iya jawo asarar rayuka.

Leadership ta wallafa cewa mabiya shi'ar sun kuma yi kira ga gwamnati da ta sakarwa jagoransu Sheikh Zakzaky da matarsa fasfo dinsu domin tafiya waje neman magani.

Kara karanta wannan

Mai gaskiya ya rantse: El-Rufai ya ce duk tsoffin gwamnonin Kaduna sun lashe kudin talakawa

Ba zan fasa rusau da korar ma'aikata ba har ƙarshen mulki na

A wani labarin mai alaƙa da wannan, an jiyo El-Rufai na cewa ba zai daina rusau da korar ma'aikata ba har zuwa ƙarshen mulkinsa.

Wannan dai na zuwa ne a cikin abinda bai kai kwanaki 10 da suka ragewa shugabannin da suke akan kujerun mulki su sauka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng