Biki Bidiri: Dangote, Tinubu, Rabiu da Indimi Sun Sayi Kwafin Litattafan Tarihin Buhari Kan N500m
- Shugaban kasa Muhammadu a kwanan nan ya kaddamar da littatafai guda biyu da suka ba da labarin rayuwarsa da mulkinsa na shekaru 8
- Fitattu a Najeriya musamman a fannin tattalin arziki sun tallafa da kudi a wajen taron bude wadannan littatafan
- Abokan Buhari wadanda suke attajirai sun saki manyan kudade domin sayen kwafin wadannan littatafai gida biyu da ya buga
Attajiran Najeriya sun yi ruwan kudi a lokacin da aka yi bikin bude littatafai guda biyu da aka rubuta game da shugaban kasa Muhammadu, rahoton jaridar Punch.
An yi bikin kaddamar da littatafan guda biyu ne a babban birnin tarayya Abuja, inda ya samu halartar manyan mutane a kasar nan.
A lokacin bikin, littatafan sun yi farin jini, domin sun samar da kudaden da basu gaza N500m ba daga hannun wadanda suka halarci taron kana suka sayi kwafi.
An yi bikin ne a cikin Banquet Hall da ke gidan gwamnati a Abuja, inda aka ga manyan mutanen duniya, ciki har da shugabar kasar Ghana Nana Akufo-Addo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Littatafan biyu sune kamar haka: "State of Repair: How Muhammadu Buhari Tried to Change Nigeria for Good," wanda Antony Goldman ya rubuta da kuma "The Legacy of Muhammadu Buhari," wanda sanata Abu Ibrahim ta rubuta.
Manufar littatafan ba komai bane face yin tsokaci ga rayuwar Buhari da kuma tasirinsa a matsayin shugaban kasan Najeriya.
Attajirai sun yi ruwan kudi
Don nuna karimci, Abdulsamad Rabiu, mai kamfanin BUA ya sayi kwafin littatafan guda biyu a kan kudi N200m.
Aliko Dangote, attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika da kuma a Najeriya ya sayi kwafin shi ma a kan kudi N100m.
Zababben shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima sun sayi kwafin a kan kudi N40m, rahoton Daily Independent.
Babban dan kasuwa a jihar Borno, Muhammadu Ndimi ya sayi kwafin wadannan littatafan a kan kudi N100m.
Haka dai aka samu manyan jiga-jigai da suka cire manyan kudade domin sayen wadannan littatafai da ake sa ran za su yi tasiri.
Mike Adenuga ya samu karayar arziki
A wani labarin, kunji yadda Mike Adenuga ya samu ragi daga dukiyarsa yayin da kasuwarsa ta dan yi sanyi a kwanan nan.
An ruwaito cewa, attajirin ya yi asarar sama da $500m cikin kasa da kwanaki 20 da aka bayyana a cikin rahotonmu na baya.
Asali: Legit.ng