"Ba Zan Fasa Korar Ma'aikata Da Rusau Ba Har Karshen Mulki Na", Gwamna El-Rufai

"Ba Zan Fasa Korar Ma'aikata Da Rusau Ba Har Karshen Mulki Na", Gwamna El-Rufai

  • Gwamnan jihar Kaduna ya sha wani muhimmin alwashi yayin da ya ke tunkarar ƙarewar wa'adin mulkinsa a ranar Litinin 29 ga watan Mayu
  • Nasir El-Rufai ya sha alwashin kakkaɓe duk wasu baragurbi a gwamnatinsa har zuwa ranar da zai yi bankwana da mulki
  • Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen ƙaɗɗamar da wani littafi a birnin Kaduna ranar Asabar, 20 ga watan Mayu

Jihar Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya sha alwashin ci gaba da korar duk wani baragurbin ma'aikaci da ya cancanci a kore shi a gwamnatinsa, da rushe duk wani gini da ya cancanci rusau har zuwa lokacin da wa'adin mulkinsa zai ƙare.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 20 ga watan Mayun 2023, a wajen bikin ƙaddamar da wani littafi wanda ya yi magana a kansa, rahoton The Nation ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Jonathan Ya Faɗi Abu 1 Da Ya Sa Shi Muggan Mafarkai Da Rashin Bacci a Lokacin Mulkinsa

Gwamna El-Rufai ya sha alwashin ci gaba da rusau a Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Littafin wanda fitaccen ɗan jarida Mr Emmanuel Ado, ya wallafa, an sanya masa sunan “Putting The People First,” cewar rahoton Daily Trust.

El-Rufai ya ce zai ci gaba da rusau ne domin kawo gyara ta yadda magajinsa, idan ya zo ba sai ya sake yi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Duk wani abinda mu ka ga bai dace ba, za mu cire shi ta yadda gwamnan da zai zo bayan mu, ba sai ya sake yi ba. Ku sanya ido ku gani har zuwa ƙarshen wa'adin lokacin da za mu bar mulki, za mu ci gaba da korar baragurbin mutane da rushe abubuwan da ba su dace ba."

Gwamnan ya bayyana hakan ne dai kwanaki kaɗan, bayan gwamnatinsa ta soke iznin mallaka na wasu kadarorin tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Makarfi, inda ta sanya musu alamar rushewa.

Kara karanta wannan

Mulki Dadi: Shugaba Buhari Ya Bayyana Muhimmin Abinda Zai Yi Kewa Sosai Bayan Ya Koma Daura

Babban Abinda Ya Sa Ban Yi Shagalin Lashe Zaben Gwamna Ba, Uba Sani

A wani labarin na daban kuma, zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana babban dalilin da ya sanya bai shirya taron murnar lashe zaɓen gwamnan jihar da ya yi ba.

Uba Sani ya bayyana cewa ya ƙi yin murnar ne saboda hankalinsa na kan sauke nauyin da aka ɗora masa na jagorantar al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng