MURIC Ta Bukaci Tinubu Ya Bai Wa Musulmai Mukaman Minista Fiye Da Kiristoci a Gwamnatinsa
- Kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta bukaci Tinubu da ya bai wa Musulmai mukaman minista fiye da Kiristoci
- A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce hakan ne kadai zai kawo daidato a wuraren da ake tauye hakkin Musulmai
- Ya ce a shiyyoyin da Musulmai suka fi yawa ya kamata Musulmai su samu ministoci shida daga cikin hudu
Abuja - Kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta bukaci zababben shugaban kasa Bola Tinubu da ya bai wa musulmai ministoci fiye da Kiristoci idan aka rantsar da gwamnatinsa.
Kungiyar ta roki Tinubu da ya bai wa Musulmai hudu a cikin shida na mukamin minista a shiyyoyin da musulmai suka fi yawa fiye da kiristoci.
Babban daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola a wata sanarwa da ya sanyawa hannu ya ce gwamnatoci da dama sun mayar da Musulmai saniyar ware a mukamai na gwamnati.
Ya ce akwai jihohi a shiyyoyin da musulmai suka fi rinjaye musamman shiyyoyi masu jihohi shida, ya kamata a bai wa Musulmai ministoci hudu sannan Kiristoci kuma su dauki biyu don samun daidaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ba da misalan da jihohin da abin ya shafa kamar jihohin Taraba da Adamawa da Bauchi a Arewa maso Gabas.
Sauran sun hada da jihohin Nasarawa Kogi da Niger a Arewa taTsakiya sai kuma Oyo da Osun da Ogun da Lagos Kudu maso Yamma da kuma jihar Kaduna a Arewa maso Yamma, cewar jaridar Vanguard.
Gwamnatocin baya sun nuna wariya ga Musumai a harkokin gwamnati
Newstral ta ce Kungiyar ta bayyana yadda gwamnatoci da dama suka nuna wariya ga Musulmai duk da rinjaye da suke dashi a wadannan yankuna, in da sanarwar ta ce a jihohi kamar su Borno da Katsina da Sokoto kadai ne ake kula da hakkin Musulmai wurin al’amuran gwamnati.
An Yankewa Ɗan Kasuwa Hukuncin Ɗaurin Wata 6 a Gidan Yari Saboda Laifin Damfarar Mai Sana'ar Tumatur
Sanarwar ta ce:
“Abin bakin ciki a jihohin Arewa kamar su Borno da Katsina da Sokoto ne kadai ake kula da hakkin Musulmai a harkokin gwamanti.
“Obasanjo da Jonathan sun ba da mukamai na ministoci ga Kiristoci kadai a yankin Kudu maso Yamma a gwamnatocinsu, sun tauye hakkin Muslmai a yankin.
“Abin da yafi muni ma shi ne yadda suka bai wa Kiristoci mukaman ministoci a wuraren da Musulmai suka fi rinjaye kamar Bauchi da Kwara da kuma Kaduna.”
Dokar kasa ta ba da daman ko wace jiha ta samu mukamin minista guda daya
A dokar kasa, ko wace jiha daga jihohi 36 da ake da su tana da daman samun mukamin minista guda daya da zai wakilceta a majalisar zartaswa.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Dalilin haka, duba da yadda za a rantsar da gwamnatin Bola Tinubu da ta yi alkawarin aiki da kowa don tabbatar da gwamnatin hadaka, muna kira da yayi duba akan irin matsalolin da gwamnatocin baya suka kawo na mai da Musulmai saniyar ware a yankunansu.
“Muna son ministoci hudu daga cikin shida a ko wace shiyya da Musulmai suka fi yawa, musamman a jihohin Taraba da Adamawa da Nasarawa da kuma Bauchi.
“Sauran sun hada da Kogi da Osun da Oyo da Ogun da kuma Niger sannan jihohin Kaduna da Lagos."
Farfesa Akintola a cikin sanarwar ya ce:
“Tabbas babu matsala idan ministoci daga Sokoto da Borno da Kano da Jigawa dukkansu Musulmai ne, haka ma idan ministoci daga Enugu da Anambra da Rivers da Cross Rivers sun kasance dukkan su Kiristoci ne, a wadannan jihohi gwamnoninsu za su iya bai wa marasa rinjaye mukamin kwamishina ko masu ba da shawara.”
MURIC Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Kirista Dan Kudu a Shugabancin Majalisar Dattawa
A wani labarin, Kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta roki dukkan Musulmai da suke neman kujerar majalisar dattawa su janyewa Kirista.
Kungiyar ta ce tana son a marawa Kirista dan Kudu baya don samun wannan mukamin a kasar ganin yadda shugaban kasa da mataimakinsa Musulmai ne.
Asali: Legit.ng