Majalisar Tarayya Ta Amince Wa Shugaba Buhari Ya Kara Karbo Bashi Bisa Sharadi

Majalisar Tarayya Ta Amince Wa Shugaba Buhari Ya Kara Karbo Bashi Bisa Sharadi

  • Majalisar tarayya ta amince shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya kara karbo bashin dala miliyan $800m
  • Sai dai 'yan majalisun sun gindaya sharadin cewa idan an karɓi bashin, a barwa gwamnatin da zata zo ta yi amfani da su
  • A ranar 29 ga watan Mayu, 2023, shugaba Buhari zai miƙa mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu

Mamban kwamitin kula da karɓo bashi a majaliaar wakilai, Abubakar Yunusa Ahmad, ya ce 'yan majalisar tarayya sun amince wa shugaba Muhammadu Buhari, ya karɓo bashin dala miliyan $800m.

Sai dai ɗan majalisar ya yi bayanin cewa sun kafa sharaɗin ba zasu bari gwamnatin Buhari mai barin gado ta kashe kuɗin baki ɗaya ba.

Muhammadu Buhari.
Majalisar Tarayya Ta Amince Wa Shugaba Buhari Ya Kara Karbo Bashi Bisa Sharadi Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

A cewarsa, gwamnatin zababben shugaban ƙasa da ke dab da kama aiki tana da haƙƙin kawo na ta tsarin yadda bashin zai amfani 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Manyan ‘Yan Siyasar da Ake Tunanin Tinubu Zai Naɗa Ministoci In Aka Rantsar Da Shi

Honorabul Ahmad, wanda ya yi jawabi a cikin shirin Sunrise Daily na kafar Channels tv ranar Jumu'a 19 ga watan Mayu, 2023, ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kuɗin dala miliyan $800m, mun tattauna sosai a kansu musamman mu da muke cikin kwamitin karɓo bashi kuma mun ba da shawarin yadda ya kamata a yi."
"Na farko, mun ce ya kamata a bar waɗan nan kuɗinn sabuwar gwamnatin da za'a kafa ta zo ta same su. Amma tunda an aminta da karɓo bashin, mai yuwuwa ba zamu iya amfani da shi duka ba."
"Wataƙila idan sabuwar gwamnati ta zo, tana da batutuwan da zata tunkara da kuɗin ba kamar wannan gwamnati mai ci ba. Mun gode Allah, rahoto ya nuna ba zata tafi da kowa a gwamnatin Buhari ba."

Tun da farko, shugaba Buhari ya aike da takarda ga majalisar dattawa, yana neman su amince ya kara sunkuto bashin dala miliyan $800m daga bankin duniya, rahoton This day ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi: Babu Wanda Zai Iya Hana Rantsar Da Tinubu

Wase: Har Yanzun Ina Cikin Tseren Kujerar Kakakin Majalisar Wakilai

A wani labarin Kun Ji Cewa 'Dan Majalisar Da Ya Lashi Takobin Yaƙar Tinubu a Majalisa Ta 10 Ya Gana da Shugaba Muhammadu Buhari a Aso Villa

Bayan ganawarsu, Ahmed Isris Wase, mataimakin kakakin majalisa ya ce har yanzun yana cikin tseren takarar kakakin majalisar wakilan tarayya ta 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262