Sojoji Sun Kai Samame Mafakar Yan Bindiga a Zamfara, Sun Halaka Da Yawa

Sojoji Sun Kai Samame Mafakar Yan Bindiga a Zamfara, Sun Halaka Da Yawa

  • Sojoji sun samu gagarumar nasara kan yan bindiga a kauyuka da dama da ke ƙaramar hukumar Shinkafi, jihar Zamfara
  • Bayanai sun nuna Dakarun soji sun kai samame sansanonin yan fashin jejin, sun halaka su da yawa, wasu sun ari na kare
  • A cewar wani jami'in hukumar soji, wannan somin taɓi ne domin ba zasu kakkauta ba har sai sun dawo da zaman lafiya a Zamfara

Zamfara - Rundunar Sojin Operation Hadarin Daji da ke aiki a Arewa Maso Yamma ta yi nasarar sheƙe 'yan bindiga da yawan gaske a ƙaramar hukumar Shinkafi, jihar Zamfara.

Dakarun sojin sun samu wannan nasara ne yayin da suka kai samame mafakar 'yan fashin dajin a garuruwa kusan 7 duk a ranakun Laraba da Alhamus, suka share duk wani abu mai rai.

Sojin Najeriya.
Sojoji Sun Kai Samame Mafakar Yan Bindiga a Zamfara, Sun Halaka Da Yawa Hoto: Army
Asali: Twitter

Yayin wannan samame, jami'an rundunar sojin sun lalata sansanon yan bindiga da ke ƙauyukan Danbokolo, Malam Ila, Malam Sale, Kagara, Gangara, Fakai da Manawa, duk a ƙaramar hukumar Shinkafi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Jami'an Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa, Sun Aiko da Sako Mai Ta Da Hankali

Wani babban jami'i a hukumar soji wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya shaida wa Channels tv cewa dakaru sun yi musayar wuta mai zafi da 'yan ta'addan a lokacin da suka kai samame.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, yayin artabu, dakarun sojin Najeriya suka yi nasarar kashe da dama daga cikin yan bindigan, wasu kuma suka ari na kare zuwa wasu Duwatsu a bayan ƙauyen Fakai ɗauke da raunukan harbi.

A kalamansa ya ce:

"Ba zamu saurara ba yanzu haka muna ci gaba da wannan aiki har sai mun kawar da yan bindiga baki ɗayansu daga jihar nan."
"Wasu da yawa sun fara tattara kayansu suna barin Zamfara sakamakon ruwan wutan rundunar soji da bama-baman sojojin sama babu kakkautawa, da zaran mun gano mafakar 'yan bindiga muke dira wurin."

Yayin wannan "Operation" dakarun soji sun kwato makamai da suka haɗa da bindigu masu haɗari kala daban-daban da kakin Soji. Haka zalika sun babbake babur, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Soke Halascin Takarar Zababɓen Gwamna da Wasu 'Yan Takara a Jihohin Kano da Abiya

Yan bindiga sun sace jami'an NRC

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ma'aikatan NRC, Sun Aiko Da Sako Mai Daga Hankali

Wasu miyagun 'Yan bindiga sun yi garkuwa da ma'aikata 2 na hukumar sufurin jiragen kasa (NRC) a Agbor, jihar Delta.

Rahotanni sun nuna maharan sun tashi hankalin mazauna yankin, kuma sun nemi maƙudan kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262