Sokoto: Tambuwal Ya Karrama Shagari, Sarkin Musulmi, Dasuki, Danfodio, da Malami

Sokoto: Tambuwal Ya Karrama Shagari, Sarkin Musulmi, Dasuki, Danfodio, da Malami

  • Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto, ya karrama wasu daga cikin manyan malamai da kuma shugabanni na jihar Sokoto
  • Ya karrama su ne dai ta hanyar sauya sunan wasu muhimman wurare da suka ƙunshi makarantu da wuraren kiwon lafiya zuwa sunayensu
  • Kwamishinan shari'a na jihar Sokoto ne ya bayar da sanarwar a yayin zama da majalisar zartarwa ta jihar a ranar laraba

Gwamnatin jihar Sokoto, karkashin jagorancin Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ta sanar da karrama wasu manyan malamai da shuwagabanni 'yan asalin jihar Sokoto.

Sanarwar dai ta zo ne ta hannun kwamishinan shari'ar jihar Sokoto, a yayin da ya ke jawabi wajen taron majalisar zartarwa ta jihar, kamar yadda Daily Trust ta yi rahoto.

Tambuwal
Tambuwal Ya Karrama Shagari, Sarkin Musulmi, Dasuki, Danfodio, da Malami. Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Gwamnati ta karrama Abdullahi Fodiyo

Gwamnatin ta sanar da sauya sunan jami’ar jihar Sokoto (SSU), zuwa sunan Sheikh Abdullahi Fodiyo, ƙanin wanda ya kafa daular Sokoto, wato Sheikh Usmanu Danfodiyo.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Kwankwaso Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Ganawar da Ya Yi da Bola Tinubu a Faransa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jami'ar Ilimi ta jahar Sokoto (SSUE), kuma an sauya na ta sunan zuwa sunan tsohon shugaban ƙasa Alhaji Shehu Shagari.

Tambuwal ya karrama Dasuki

Haka nan kuma gwamnan ya karrama marigayi Sultan Ibrahim Dasuki, inda ya sauya sunan kwalejin ilimi ta Shehu Shagari (SSCOE) zuwa sunansa.

Sannan, gwamna Tambuwal ya karamma Ambasada Shehu Malami, sarkin Sudan ɗin Wurno, wanda kuma shi ne tsohon babban kwamishinan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu, ta hanyar canza sunan kwalejin noma da kiwon dabbobi (CAAS), da ke Wurno zuwa sunansa.

An karrama Sheikh Halliru Binji

Kwalejin shari’a da nazarin addinin Musulunci ta Wamakko (CLIS), ita kuma an sauya sunanta zuwa Sheikh Haliru Binji College of Law and Islamic Studies, a yayin da kwalejin jinya ta Tambuwal, aka canja sunanta zuwa Balaraba Buda.

Kwamishinan shari’a na jihar Sokoto, Suleiman Usman (SAN) ne ya bayyana haka a wajen taron majalisar zartarwa ta jihar Sokoto da gwamnan ya jagoranta a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Yi Fatali da Shirin Gwamnonin Arewa 5, Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Baya a Majalisa Ta 10

Buhari zai karrama Tinubu da Shetima

A wani labarinmu na baya, kun ji cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari mai barin gado ya bayyana cewa zai karrama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shetima.

Buharin ya ce zai karramasu ne da lambobin yabo gabanin ya bar ofis a ranar 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng