Jerin Taro, Wasanni da Shagulgulan Mika Mulki 12 da Za a Shirya na Tsawon Kwana 7
- An shirya taro da liyafa da bukukuwa dabam-dabam a shirye-shiryen rantsar da shugaban kasa
- Boss Mustapha ya sanar da abubuwan da aka yi tanadi kafin Muhammadu Buhari ya mika mulki
- Za a yi wadannan taro ne a Aso Rock, Masallacin kasa, Coci, Farfajiyar Eagle da sauran wurare
Abuja - Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya ce akwai taro da liyafa da lacca da za a gabatar duk a cikin shirye-shiryen rantsar da shugaban kasa.
Premium Times ta ce za a dauki mako guda ana shagulgula a birnin Abuja.
Zababbun shugabanni su na samun mafi girmar lambar yabo, a 2010 ne aka saba ka’ida da Goodluck Jonathan ya hau mulki, za ayi irin haka a wannan karo.
Dr. Goodluck Jonathan ya samu mulki ne bayan rasuwar Ummaru Yar’Adua, sai majalisar koli ta ba shi lambar yabon da ya zama sabon shugaban Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Talata 23 ga watan Mayu 2023
Liyafa da za a shirya domin karrama Shugaban kasa
A gidan sojoji da karfe 7:00 na dare.
Laraba 24 ga watan Mayu 2023
Wednesday, 24th May 2023
Taron majalisar FEC na karon karshe
A dakin taron majalisar a fadar shugaban kasa
Alhamis, 25 ga watan Mayu 2023
Karrama zababben shugaban kasa da mataimakinsa da lambobin girman GCFR da GCON da kuma mika takardun karbar gwamnati
A babban dakin taro na fadar shugaban kasa da karfe 10:00 na safe.
(Masu halarta za su zauna da karfe 9:00ns)
Juma’a, 26 ga watan Mayu 2023
Lacca ta musamman da sallar Juma’a
Babban masallaci da karfe 10:00ns da 1:30nr
Lacca a kan karfafa damukaradiyya wanda Mai girma tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru M. Kenyatta zai gabatar
A babban dakin taro na kasa da karfe 10:00ns
(Masu halarta za su zauna da karfe 9:00ns)
Asabar 27 ga watan Mayu 2023
Taron ranar yara
I. Fareti
II. Liyafar yara
A tsohon filin farteti da karfe 10:00ns
A dakin taron fadar shugaban kasa da karfe 2:00nr
Lahadi 28 ga watan Mayu 2023
Zaman coci
A babban cocin kasa da karfe10:00ns
Liyafar rantsuwa/Daren gala
Dakin taron fadar shugaban kasa 7:00ns
Litinin 29 ga watan Mayu 2023
Faretin rantsuwa/mika mulki
Farfajiyar Eagle Square, CBD da karfe10:00ns
Liyafar bayan rantsuwa
Fadar shugaban kasa da karfe 1:30 (za a shiryawa shugaban kasa, takwarorinsa da sauran shugabanni da wadanda aka gayyata).
Lambobin GCFR da GCON
Kafin Muhammadu Buhari ya mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, an ji labari zai bada lambar yabo ga zababben shugaban kasa da mataimakinsa.
Baya ga lambar yabo na GCFR da GCON da Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima za su samu, Premium Times ta ce akwai abubuwa iri-iri da za ayi.
Asali: Legit.ng