Tsohon Minista Ya Shiga Ha’ula'i Shekara 1 da Barin Ofis, Kotu Ta Amince a Cafke Shi

Tsohon Minista Ya Shiga Ha’ula'i Shekara 1 da Barin Ofis, Kotu Ta Amince a Cafke Shi

  • Gwamnatin da Nyesom Wike yake jagoranta ta na shari’a da Gwamnatin Rotimi Amaechi a kotu
  • Ana tuhumar tsohon Gwamnan Ribas da waninsa da cefanar da wasu kadarorin da Jiharsa ta mallaka
  • Ganin sun ki zuwa kotu domin su kare kan su, wani Alkali ya yarda a kama Amaechi da Tony Cole

Rivers – A tsakiyar makon nan, wata babbar kotun jiha mai zama a garin Fatakwal a jihar Ribas ta bada dama a damke Rotimi Amaechi da Tonye Cole.

The Cable ta ce Alkalin babban kotun jihar ya amince a cafke tsohon Ministan sufurin da Tonye Cole wanda ya yi wa APC takarar Gwamna a Ribas.

Alkalin da ya bada wannan umarni, Chinwendu Nwogu ya samu wadanda ake tuhuma da laifin kin bayyana a gaban kotu a shari’ar da ake yi da su.

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Cigaba da Fitowa Kan Mutanen da Tinubu Zai Ba Mukamai a Gwamnati

Tsohon Minista
Rotimi Amaechi yana Minista Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Rahoton ya ce Gwamnatin Ribas ta yi karar Tonye Cole da uban gidansa, Rotimi Amaechi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamfanonin da ake bincike

Gwamnati ta na shari’a da kamfanin Sahara Energy Resources Limited, kamfanin Chamberlain Peterside da kuma NG powers HPS Limited a kotu.

Haka zalika an yi karar wani kamfani mai suna Cenpropsaroten Management Ltd saboda ayyukan da aka yi a lokacin Amaechi yana kan mulki.

Wike ya na zargin tsohon ubangidansa a siyasa ya yi facaka da dukiyar gwamnatin Ribas a yayin da ya yi shugabanci tun daga 2007 har zuwa 2015.

Za a koma kotu a Yuli

A karshen zaman da ak ayi, Alkali ya daga karar sai zuwa 5 ga watan Yulin 2023.

Daily Post ta ce zargin ne ya jawo aka kafa kwamitin mutum bakwai da ya binciki Naira biliyan 96 da aka cire daga baitul-mali a gwamnatin baya.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Amurka Tayi wa Najeriya da Sakataren Gwamnati Ya Kira Tinubu a Waya

Kwamitin ya yi bincike a kan zargin saida kadarori da gwamnatin baya tayi a Ribas.

Daga cikin kadarori masu daraja da ake tunanin an saida akwai wasu kayan aikin wuta na Omoku, Afam, Trans Amadi, Eleme da wani katafaren otel.

Da aka bijiro da batun cefanar da dukiyoyin gwamnati, Chinwendu Nwogu bai saurari rokon Lauyoyin wadanda ake kara ba, ya yi izini a kamo su.

Za a tono jan aiki

Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya fadawa Hukumar EFCC ta binciki Ministoci da jami’an Aso Rock, a ranar Alhamis mu ka fitar da wannan rahoto.

Gwamnan jihar Zamfara ya ce dole ne EFCC ta binciki har da Ministocin da za su bar mulki, yana ganin babu adalci a ce Gwamnoni kurum za a tasa a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng