Gwamnan APC Ya Zugo Hukumar EFCC Ta Binciki Duka Mukarraban Gwamnatin Buhari

Gwamnan APC Ya Zugo Hukumar EFCC Ta Binciki Duka Mukarraban Gwamnatin Buhari

  • Gwamnan Zamfara ya na so Hukumar EFCC ta binciki jami’an gwamnatin tarayya da za su bar ofis
  • Bello Muhammad Matawalle ya fitar da jawabi bayan ya ji za a soma binciken Gwamnatocin Jihohi
  • Mai girma Gwamnan ya na ganin bai kamata aikin EFCC ya tsaya a jihohi ba, a shiga har Aso Rock

Zamfara - Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara, ya yi kira ga EFCC ta binciki jami’an gwamnatin tarayya da za su sauka daga mulki.

A ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto Bello Muhammad Matawalle ya na bada shawarar ayi bincike kan Ministoci da jami’an fadar shugaban kasa.

Gwamnan jihar Zamfara ya yi wannan kira ne a matsayin martani bayan ya ji Abdulrasheed Bawa yana cewa EFCC ta aikawa Gwamnoni gayyata.

Gwamnan APC
Bello Matawalle da Gwamnonin APC a Aso Rock Hoto: punchng.com
Asali: UGC

EFCC vs Gwamnonin Najeriya

Kara karanta wannan

‘Yan PDP, LP da NNPP Fiye da 100 Su Na Goyon Bayan ‘Dan Takaran APC a Majalisa

Shugaban Hukumar EFCC ya fitar da jawabi, ya nuna za su soma binciken Gwamnonin jihohi da Kwamishinonin da za su bar karagar mulki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bello Matawalle yana ganin bai dace binciken ya tsaya a jihohi ba, ya kuma bada shawarar ka da a siyasantar da lamarin yaki da barayin gwamnati.

"Hankali na ya je ga wani jawabi da aka ce ya fito daga wajen shugaban hukumar EFCC, Malam Abdulrasheed Bawa inda aka ji ya na ikirarin sun aika gayyata ga duka Gwamnoni da Kwamishinoni da za su bar ofis domin su fara binciken zargin rashin gaskiya da suka tafka a ofis.
Ko da hakan daidai ne kuma abin a yaba domin ya na da kyau a san abubuwan da jami’an gwamnati suka yi a mulki, kuma EFCC ta na da ikon yin bincike.
Sai dai ya kamata a bi doka sau-da-kafa wajen binciken. Dole a binciki kowa kuma ka da a ware wasu.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Yana Landan, Osinbajo Ya Amince a Kafa Sababbin Jami’o’i 36 a Najeriya

A haka ne na ke cewa babu adalci, akwai munafunci kuma an nuna bambanci babu gaira-babu dalili wajen wannan gayyata da hukumar EFCC ta fara.

Jaridar Premium Times ta rahoto Gwamnan ya na mai cewa wannan rashin adalci da ake yi a karkashin jagorancin Bawa zai maida hannun agogo baya.

Ganin Matawalle ya bukaci EFCC ta binciki duka jami’an fadar shugaban kasa da ‘yan majalisar FEC, sai aka samu labari gwamnatin tarayya ta tanka.

A wani rahoton an ji da aka nemi Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya yi magana, sai ya ce ai Gwamnan ya na da damar fadin ra’ayinsa.

FEC ta yi zama na musamman

A karshen wa’adin mulkin Gwamnati mai-ci, rahoto ya zo cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya amincewa ‘Yan kasuwa gina wasu Jami’o’i 37 a kasar nan.

Yemi Osinbajo ya dauki wannan mataki a wajen taron FEC a fadar Aso Rock, hakan ya na nufin adadin Jami’o’in kasuwa da ake da su ya zarce 70 kenan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng