Gwamnatin Amurka Ta Yi Martani Kan Harin Da Aka Kai Kan Jami'anta a Jihar Anambra
- Gwamnatin Amurka ta fito fili ta yi martani kan harin da aka kai kan jami'an ofishin jakandancinta a jihar Anambra
- Gwamnatin ta bayyana cewa harin bai ritsa da ɗan ƙasar Amurka ko ɗaya ba, saboda haka ba ɗan ƙasar ko ɗaya da ya mutu
- Gwamnatin ta kuma bayyana cewa tana nazari kan mummunan harin da aka kai kan jami'an na ta
Washington - Fadar gwamnatin Amurka ta White House, ta yi magana kan mummunan harin da aka kai kan wasu jami'an ofishin jakadancin Amurka na Najeriya a jihar Anambra, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
A yammacin jiya Talata ne dai, aka kai harin kan kwamban jami'an ofishin jakadancin a ƙaramar hukumar Ogbara ta jihar Anambra.
Mutum huɗu ne dai suka rasa ransu a harin da aka kai, inda maharan kuma suka yi awon gaba da wasu jami'an ƴan sanda mutum biyu, da wani direba.
Da ya ke tabbatar da aukuwar lamarin, a yayin ganawa da manema labarai, kakakin majalisar zartaswar tsaron Amurka, John Kirby, ya ce babu ɗan ƙasar ko ɗaya da ya halaka a harin, cewar rahoton The Caɓle.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
"Sai da na samu bayanai sosai kafin na fito nan na yi magana da ku. Ya yi kama da cewa an farmaki kwamban motocin Amurka."
"Abinda zan gaya mu ku shine babu ɗan ƙasar Amurka ko ɗaya a ciki, saboda haka babu ba amurke ko ɗaya da ya raunata."
"Amma muna sane da cewa an samu raunika, tabbas har wasu ma sun rasa ransu, amma ba na son na yi dogon bayani sosai a yanzu."
Kirby ya kuma ƙara da cewa suna yin duba kan harin da ya auku.
Alkawarin da Amurka Tayi wa Najeriya da Sakataren Gwamnati Ya Kira Tinubu a Waya
Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Budewa Jami'an Ofishin Jakadancin Amurka Wuta a Anambra, Sun Halaka Mutane Da Dama
A wani labarin na daban kuma, sakataren gwamnatin Amurka ya kira zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a wayar tarho, inda suka ɗauki dogon lokaci suna zantawa.
A yayin zantawar ta su, Anthony Blinken, ya shaidawa Tinubu cewa Amurka a shirye ta ke ta ba shi dukkanin haɗin kan da ya ke buƙata domin ƙara ƙarfafa alaƙar da ke a tsakanin ƙasashen biyu.
Asali: Legit.ng