Jerin Jami'o'in Duniya Na 2023: Sunayen Jami'o'in Najeriya Da Suka Shiga Cikin Jerin Na Bana

Jerin Jami'o'in Duniya Na 2023: Sunayen Jami'o'in Najeriya Da Suka Shiga Cikin Jerin Na Bana

  • Aƙalla jami'o'i huɗu na Najeriya ne suka shiga cikin jerin jami'o'in duniya 2,000 kamar yadda cibiyar tantance jami'o'i ta duniya CWUR ta sanar
  • Dina Elsayed, ta bayyana a cikin wata sanarwa da cibiyar ta fitar, cewa darajar wasu jami’o’in Najeriya ta ƙaru ne saboda yawan bincike da suke yi
  • Cibiyar ta ce an yi amfani da abubuwa huɗu ne wajen tantance jami’o’in, waɗanda suka haɗa da bincike, daukar ma’aikata, sassan karatu da kuma matakin ilimi

Cibiyar tantance jami'o'i ta duniya CWUR ta wallafa jerin sunayen jami'o'i 2,000 mafi inganci da daraja a duniya, bayan wallafa jami'o'i 20,531 na duniya da ta yi.

Kamar yadda cibiyar ta wallafa a shafinta na yanar gizo, jami'o'in Najeriya huɗu ne suka samu damar shiga cikin jerin jami'o'i mafi inganci a duniya.

An dai wallafa bayanan jami'o'in da suka fi ingancin ne a ranar Litinin, 15 ga watan Mayun da muke ciki.

Kara karanta wannan

Dan Majalisar APC Ya Hango Wani Babban Kuskure Da Jam'iyyar Za Ta Yi Kan Shugabancin Majalisa ta 10

Nigerian Uni
Sunayen Jami'o'in Najeriya Da Suka Shiga Cikin Jerin Na Duniya Na Bana. Hoto: Nigerian Universities
Asali: Twitter

Matakan da aka bi wajen tantance jami'o'in

Kamar dai yadda cibiyar tantancewar ta fitar da sanarwa, 'yar jarida Dina Elsayed kuma ta aikawa da Legit.ng kwafi wanda ke bayyana cewa jami'o'in Najeriya sun samu ƙarin matsayi ne sakamakon yawan bincike da suke yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'ar Harvard dai ita ce jami'ar da ta fi kowace inganci a duniya. Kaso 96% na jami'o'in kasar Sin suma sun samu ƙarin matsayi sakamakon yadda ƙasar ke ƙara kashe kuɗaɗe a makarantunta.

Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa, an gudanar da tantancewar ne bisa la'akari da abubuwa guda huɗu da suka haɗa da bincike, matakin ilimi, ɗaukar ma'aikata, da kuma yawan sassan karatu.

Akwai buƙatar a ƙara wadata makarantun Najeriya da kuɗaɗe

Shugaban cibiyar binciken na ƙasa Dr Nadin Mahassen, ya bayyana cewa abin farin ciki ne ganin yadda jami'o'in Najeriya ke ƙara samu ci-gaba a matakai na duniya.

Kara karanta wannan

Majalisa ta 10: Daga Karshe Gwamnonin APC Sun Shirya Kawo Mafita Kan Rigimar Shugabancin Majalisa

Ya ƙara da cewa dole ne a ƙara ƙaimi wajen kashewa makarantun kuɗi don inganta harkokin koyo da koyarwa a cikinsu.

Ya ce hakan in aka yi, zai taimaka wajen ƙara samun ɗalibai da kuma malamai masu hazaƙa waɗanda sune ke ɗaga darajar makaranta.

Ga dai jerin sunayen manyan jami'o'in Najeriya huɗu da suka samu shiga, da kuma taƙaitaccen bayani kan kowace daga cikinsu.

  • University of Ibadan, UI

Jami'ar Ibadan itace jami'a ta ɗaya a Najeriya, sannan kuma ta 1163 a duniya. Ta samu nasarar hawa kan jami'o'i tara daga matakin da ta ke a baya.

  • University of Nigeria Nsukka

Jami'ar Nsukka da ke jihar Enugu ita ce jami'a ta biyu a Najeriya, sannan kuma ita ce ta 1784 a duniya. Jami'ar ta dawo ƙasan wasu jami'o'i tara da ta ke samansu a baya.

  • University of Lagos

Jami'ar Legas ita ce jam'ia ta uku a Najeriya, sannan kuma ta 1875 a duniya. Ta hau saman jami'o'i 49 zuwa matsayin da ta ke a yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini

  • Ahmadu Bello University Zaria

Jami'ar ABU da ke Zaria, ita ce jami'a ta huɗu a Najeriya, sannan kuma ta 1881 a cikin jerin jami'o'im duniya.

An jibge jami'an tsaro a jami'ar Gusau

A wani labarin namu na baya, kun ji cewa an jibge jami'an tsaro a jami'ar gwamnatin tarayya da ke Gusau jihar Zamfara.

Hakan dai ya biyo bayan wasu ɗalibai mata guda biyu da masu garkuwa da mutane suka ɗauke a rukunin gidajen kwanan ɗaliban jami'ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng