Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dagaci da Wasu Mutane 3 a Jihar Niger
- Rundunar ‘yan sandan jihar Niger ta tabbatar da sace dagacin kauyen Dugge a karamar hukumar Rijau ta jihar
- Kakakin rundunar DSP Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da haka a wata sanarwar da ya fitar a jiya Litinin
- Ya ce bayan sace dagacin kauyen Dugge, ‘yan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutane da dama a yankin
Jihar Niger - Rundunar ‘yan sandan jihar Niger ta tabbatar da sace dagacin kauyen Dugge Alhaji Abdullahi B. Zaure da ‘yan bindiga suka yi a karamar hukumar Rijau dake jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa inda ya ce ‘yan bindigan sun sace dagacin kauyen da wasu mutane guda tara amma lokacin da sojoji suka kai dauki, mutane hudu daga cikinsu sun kubuta.
Jaridar Daily Trust ta tattaro yadda ‘yan bindiga suka durfafi kauyukan karamar hukumar, suka sace mutane da dama da kuma kora shanu da dama a makon da ya gabata.
Irin barnar da aka yi
Ya kara da cewa an sace shanu 60 a harin da aka kai ranar 10 ga watan Mayu yayin da mutane uku suka ji rauni.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin ya kara da cewa:
“An kai hari a bayan garin kauyen Shambo da Genu da Tungan-Bunu da Jama’are da kuma Sabon Garin karamar hukumar Rijau.
“A lokacin harin, an sace dagacin kauyen Dugge Alhaji Abdullahi B. Zaure yayin da mutane uku suka samu raunuka, an dauki wadanda suka samu raunin zuwa babban asibitin Tungan-Magajiya don basu kulawa."
Kakakin ya tabbatar da cewa jami’an ‘yan sanda suna iya kokarinsu don ganin an kubutar da sauran wadanda aka sacen, cewar rahoton gidan talabijin na Channels.
Nasara: Yan Sanda Sun Yi Nasarar Sheke Kasurgumin Dan Bindiga a Jihar Kaduna
A wani labarin, 'yan sanda a jihar Kaduna sun ce jami'ansu sun samu nasarar bindige wani okasurgumin dan ta'adda da ya addabi yankunan jihar, bayan artabu da suka yi da shi.
Bayan nasarar hallaka dan bindigan, jami'an 'yan sandan sun kuma kwace babur wanda 'yan bindigan suke amfani da shi wurin kai hare-harensu musamman a kauyen Kidandan na kudancin jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng