Rundunar ’Yan Sanda Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ta Sanya wa Seun Kuti Ankwa Bayan Ya Mika Kansa
- Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta bayyana dalilin sanya wa Seun Kuti ankwa bayan ya mika kansa
- Kakakin rundunar Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter a ranar Litinin 15 ga watan Mayu
- Ana zargin Kuti da cin zarafin jami'in dan sanda a bakin aiki a ranar Asabar 13 ga watan Mayu bayan yaduwar wani bidiyo
Jihar Lagos - Rundunar ‘yan sandan jihar Lagos ta bayyana dalilin da yasa suka sanya wa mawaki Seun kuti ankwa duk da cewa shi ya mika kansa ga jami’ansu.
An kama mawaki Seun Kuti wanda 'da ne ga tsohon mawaki Fela Ranson Kuti a ranar Litinin 15 ga watan Mayu bisa zargin cin zarafin jami’in dan sanda a bakin aiki a ranar Asabar.
An gano hotunan mawakin lokacin da jami’an ‘yan sanda suka kamashi zuwa ofishinsu, cewar jaridar Daily Trust.
Mutane da dama a ranar Litinin 15 ga watan Mayu sun yi ta korafi a kafar sada zumunta ta Twitter inda suka soki jami’an 'yan sandan kan sanya wa Kuti ankwa a hannunsa duk da mika kansa da ya yi ga rundunar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma a martanin da rundunar ta mayar ta bakin kakakinta na jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya bayyana dalilin sanya wa Kuti ankwa.
Hundeyin ya wallafa a shafin Twitter cewa:
A cewarsa:
“Saboda doka ta bamu damar mu sanya wa duk wani mai laifi ankwa da yake jawo tashin hankali kuma don kada mu kaucewa yin adalci."
A kwamushe mana Kuti, inji IGP
Idan baku manta ba sifetan ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba shi ne ya bai wa kwamishinan ‘yan sandan jihar umarnin kama mawakin a ranar Asabar 13 ga watan Mayu.
An ba da umarnin ne bayan gano wani faifan bidiyo da ya yadu a kafar sada zumunta inda mawaki Seun Kuti ya mari jami’in dan sanda a bakin aiki a ranar asabar 13 ga watan Mayu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa bayan yaduwan faifan bidiyon sai aka nemi mawakin aka rasa ya gudu maboya.
Zanga-Zanga: 'Yan sanda sun Kama Sowore a Abuja
Yan sandan a Najeriya sun cafke mawallafin Sahara reporters, Omoyele Sowore a bisa jagorantar wata zanga-zanga da yayi a babban birnin tarayya na Abuja.
An kama Sowore da wasu 'yan gwagwarmaya bayan da suka fito zanga-zanga mai suna #CrossoverWithProtest, wadda suka shirya a dukkan fadin kasar.
Asali: Legit.ng