CrossoverWithProtest: 'Yan sanda Najeriya sun cafke Omoyele Sowore

CrossoverWithProtest: 'Yan sanda Najeriya sun cafke Omoyele Sowore

- 'Yan sandan Najeriya sun damke Omoyele Sowore a kan wata sabuwar zanga-zanga da ya fito

- An damke shi a babban birnin tarayya bayan bayyana a zanga-zangar #CrossoverWithProtest

- Tun a ranar Alhamis yayi wallafa a shafinsa na Twitter a kan gangamin a dukkan kasar nan

'Yan sandan Najeriya sun sake damke mawallafin Sahara reporters, Omoyele Sowore a kan jagorantar wata zanga-zanga da yayi a babban birnin tarayya na Abuja.

Sowore tare da wasu 'yan gwagwarmaya sun shiga hannun 'yan sandan bayan da suka fito zanga-zanga mai suna #CrossoverWithProtest, zanga-zangar da suka shirya a dukkan fadin kasar nan ana gobe sabuwar shekara.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka arce ne suka tabbatarwa da Premium Times cewa an damke Sowore inda aka jefa shi daya daga cikin motocin 'yan sanda bakwai da aka tura wurin zanga-zangar.

KU KARANTA: 2023: Afenifere ta bayyana matakin da ta dauka idan Jonathan ya fito takara

An kuma: 'Yan sanda Najeriya sun cafke Omoyele Sowore
An kuma: 'Yan sanda Najeriya sun cafke Omoyele Sowore. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

Duk da majiyoyin basu san inda aka yi da Sowore ba, Sahara Reporters ta ce yana ofishin 'yan sanda na mayanka da ke Lokogoma a Abuja tare da wasu.

Hakazalika, an yi ta kokarin samun Sowore ta lambar wayarsa amma abun ya ci tura a safiyar Juma'a.

Har a lokacin rubuta wannan rahoton, ba a san mutane nawa bane 'yan sandan suka cafke yayin zanga-zangar ba.

Tun dai a safiyar Alhamis ne Sowore yayi kira ga 'yan Najeriya da su fito zanga-zangar tare da daukar kyandira da fastoci inda za su nuna alhininsu a kan mulkin Buhari.

Frank Mba, kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya bai daga wayarsa ba yayin da ake ta kiransa domin jin tsokacinsa.

KU KARANTA: Iko sai Allah: Matar aure dauke da cikin tagwaye ta sake samun wani cikin

A wani labari na daban, Sarkin Kauran Namoda a jihar Zamfara, Manjo Sanusi Muhammad Asha ya musanta ikirarin rundunar 'yan sandan jihar Katsina inda suka ce sune suka cece shi yayin da 'yan bindiga suka kai masa hari a kan titin Zaria zuwa Funtua.

Sarkin ya sanar da Daily Trust cewa a yayin da aka kai masa hari kusa da garin Maska, babu dan sanda ko daya a yankin.

"A yayin da wasu daga cikinmu suka tsere, tawagata ta karasa wani kauye da ake kira Kwanar Maska inda muka tambaya ko akwai 'yan sanda amma suka ce babu sai mun karasa Funtua."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng