Kwanaki 13 Kafin Ya Bar Aso Villa, Buhari Ya Fadi Kokari 3 da Ya Yi Cikin Shekaru 8

Kwanaki 13 Kafin Ya Bar Aso Villa, Buhari Ya Fadi Kokari 3 da Ya Yi Cikin Shekaru 8

  • Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi a gaban Gwamnonin da ke barin mulki da masu jiran gado
  • Shugaban Najeriya zai bar ofis nan da ‘yan kwanaki, ya nuna ya samu kalubale a gwamnatinsa
  • Mai girma Buhari ya nuna inda aka ci karo da cikas da kuma wasu nasarori da gwamnati ta samu

Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tuna da shekaru kusan takwas da gwamnatinsa ta shafe a mulki, ya ce ba sumul abubuwa suka tafi ba.

Mai girma Muhammadu Buhari ya nuna duk da kalubalen da aka samu, ya daura tubalin kawowa Najeriya cigaba, This Day ta fitar da wannan rahoton.

Shugaban kasar ya yi wannan magana ne da yake karanto jawabinsa a wajen taron da kungiyar gwamnoni na kasa ta NGF ta shirya jiya a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Ku Cika Alkawuran Da Kuka Dauka Ko A Yi Waje Da Ku, Buhari Ya Shawarci Gwamnoni

Aso Rock
Taron Ministoci a Aso Rock Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya karanto jawabin a madadin Mai girma Muhammadu Buhari ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabin da Farfesa Gambari ya karanto, ya ce gwamnatin tarayya ta samu nasarori daga 2015 zuwa yau, amma an ci karo da wasu kalubale a hanya.

Da yake ba kan shi maki, shugaban kasa mai jiran gado ya ce gwamnatinsa tayi abin a yaba ta fuskar gina abubuwan more rayuwa, noma da kuma tsaro.

Jawabin Mai girma Muhammadu Buhari

“Mun yi ta samu cigaba daga lokacin da mu ka shiga ofis a 2015. Akwai gargada a hanyar saboda yanayin matsalar kudi.
Amma ina mai alfahari yayin da za mu bar mulki nan da makonni biyu cewa mun kafa tubali na kawo cigaba a Najeriya.
Ba za mu iya yin komai ba, amma mun maida hankali a bangarorin abubuwan more rayuwa, harkar gona da kara karfin soja.

Kara karanta wannan

Pantami da Wasu Ministocin Buhari 9 Da Za Su Iya Tsira da Kujerunsu a Mulkin Tinubu

- Muhammadu Buhari

Wadanda suka yi jawabi a taron

Manyan da suka yi jawabi a wajen zaman da NGF ta shiryawa Gwamnoni masu jiran gado sun hada da Shugabar WTO watau Dr. Ngozi Okonjo-Iweala.

Sun ta ce saura sun hada da Mataimakiyar shugabar majalisar dinkin Duniya, Amina Mohammed, Bukola Saraki, David Greene da kuma Tony Elemelu.

Aiki a gaban Tinubu

Ku na da labari Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya na shirin gadon ragargajajjiyar Naira, rashin aikin yi da tsadar kayan abinci da na masarufi a Najeriya.

Daga cikin abubuwan da za su ba Gwamnati mai zuwa ciwon-kai akwai samar da isasshen wutar lantarki, bayan nan akwai batun janye tallafin mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng